
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI a Abuja
Wakilin Babban Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman ga kula da Yammacin Afirka da yankin Sahel, Leonardo Santos Simão, ya bayyana baƙin cikinsa game da mummunan fashewar wata tankar man fetur a garin Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura a Jihar Jigawa.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 17 ga watan Oktoba, Simão ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma gwamnati da al’ummar Nijeriya baki ɗaya.
Fashewar, wadda ta auku cikin mummunan yanayi, ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 150 tare da jikkata wasu da dama, lamarin da ya yi matuƙar barna.
Simão ya kuma yi fatan samun sauƙi cikin gaggawa ga waɗanda iftila’in ya shafa.
