Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya miƙa sunayen sababbin ministoci ga Majalisar Dattijai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Dattijai ta karɓi sabbin sunayen ministoci bakwai da da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana su a ranar Laraba don tantancewa.

Shugaba Tinubu ya aika da saƙon ne ga Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio wanda aka karanta shi a zaman Majalisar na ranar Alhamis.

Sunayen ministocin sune kamar haka; Dakta Nantawe Yilwatda, Ministan Jin-ƙai da Rage Talauci; Muhammadu Maigari Dingyaɗi, Ministan Ƙwadago da Ɗaukar aiki; Bianca Odinaka Odumegu-Ojukwu, Ƙaramar Ministar Harkokin Waje; Dakta Jumoke Oduwole, Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Ci-gaba; Idi Muktar Maiha, Ministan Ci-gaban Kiwo; Rt Hon. Yusuf Abdullahi Ata, Ƙaramin Ministan Gine-gine; da kuma Dakta Suwaiba Sa’id Ahmad, Ƙaramar Ministar Ilimi.

A halin yanzu dai, Shugaba Tinubu na jiran Majalisar ta yi nazari game buƙatar ta tabbatar da sabbin ministocin waɗanda Akpabio ya ce Majalisar ta miƙa batun ga kwamitin baki ɗaya wanda ake sa ran zai fitar da sakamakonsa nan ba da jimawa ba.

By Babaji