Darasi daga iftila’in fashewar tankar mai a Majiya

Spread the love

Fashewar tankar mai da ta afku a garin Majiya da ke ƙaramar Hukumar Taura ta jihar Jigawa da tsakar daren ranar Talata 15 ga watan Oktoba, 2024, ta yi muni matuƙa. Babbar motar dakon mai da ta taso daga Kano zuwa Nguru a jihar Yobe ta yi hatsari, inda man ya kwarara cikin wata magudanar ruwa da ke kusa da wurin. Kimanin mutane 250 ne suka taru domin ɗiban man fetur ɗin a lokacin da tankar ta kama da wuta, lamarin da ya haifar da mummunar illa. An samu ƙonewar fiye da rabin mutanen, wasu kuma ba a iya gane su ba, yayin da kimanin 100 ke kwance a asibiti sakamakon mununan raunukan da suka samu. Alƙaluman hukumar NEMA sun nuna cewa an binne gawarwakin mutane 147 a wani ƙabarin bai-ɗaya a ranar Laraba. ƙila adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa yanzu. Gwamna Umar Namadi ya bayyana lamarin a matsayin babban abin takaici da ya afku a jihar, wanda kowa ya yarda da hakan. Mutanen ƙaramar garin waɗanda akasarinsu manoma ne da ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu za su cigaba da tunawa da wannan lamari har tsawon rayuwarsu. Mu a Blueprint Manhaja mun jajanta musu; mun ji raɗaɗin da suka ji.

A yayin da ake ta ta’aziyya da ba da gudunmawar agaji daga gwamnatoci da ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun jama’a, dole tambaya ta taso ta cewa ko za a ɗauki darasi daga wannan bala’in? Duk da cewa hukumomi irinsu Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa (FRSC), da Hukunar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur (NMDPRA) da Hukumar Binciken Lafiyar Nijeriya (NSIB) duk sun fara gudanar da bincike kan fashewar tankar man, ya zama dole a jawo hankali sosai kasancewar fashe-fashen tankokin man da aka saba gani a Nijeriya, amma abin da ke biyo baya yana da ban tsoro. A yankin Neja-Delta mai arzikin man fetur ɗaruruwan mutane ne suka mutu sakamakon tashin wuta a sanadin mai a lokuta daban-daban, yayin da suke ƙoƙarin fasa bututun mai, wanda a wasu lokutan wasu marasa kishin ƙasa ke ɗaura mugun nufin satar man. Hakazalika motoci dakon mai sun kashe ɗaruruwan mutane a sassan ƙasar ko dai a lokacin da suke ɗiban mai ko kuma lokacin da tankokin suka yi haɗari a cikin al’umma. A mafi yawan lokuta, baya ga mace-macen, an yi asarar dukiyoyi da dama. ƙasa da watanni biyu da suka gabata a cikin watan Satumba mutane 59 ne suka mutu a jihar Neja bayan da wata tankar mai ta yi karo da wata babbar mota mai ɗauke da fasinjoji da shanu. Kuma a daidai lokacin da ake gudanar da jana’izar jama’a a garin Majiya a safiyar ranar Laraba, wata tankar mai ɗauke da mai ta kife a kan babban titin garin Ibafo na jihar Ogun, inda ta yi ta zubar da mai sannan man ya kama da wuta. Duk da cewa ba a yi asarar rayuka ba, dukiyoyi na miliyoyin naira sun lalace.

Duk da faruwar waɗannan lamurra, babu wanda ya damu game da ɗaukar matakan kariya don gujewa faruwar hakan a nan gaba. A duk lokacin da irin waɗannan haɗurran suka faru, hukumomin gwamnati su kan garzaya da irin waɗannan kalamai da aka saba yi, yayin da mutanen da abin ya shafa ke gaggauta komawa harkokinsu na yau da kullum. Me ya sa muke mantuwa haka?

Akwai buƙatar a ɗauki wasu matakai domin magance waɗannan fashe-fashen tankoki da ke faruwa. Na farko, a fili yake mafi yawan jama’a sun jahilci illar da ke tattare da ɗiban mai daga tankunan da suka faɗi, ta yadda za su haifar wa kansu haɗari. Hukumomin gwamnati da abin ya shafa da suka haɗa da hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa (NOA), ya kamata su fara bayar da shawarwarin wayar da kan ‘yan Nijeriya irin waɗannan haɗurran. Na biyu, ya kamata gwamnati ta ci gaba da magance matsalar talauci, musamman a matakin farko. Idan ba don rashi da talauci ke haifarwa ba, ta yaya ɗaruruwan mutanen da ya kamata su kwanta barci za su garzaya da guga da sauran kwantena don ɗibar mai daga motar da ta yi haɗari da tsakar dare?

Wani matakin kariya kuma yana da alaƙa da tura ‘yan sanda da ma’aikatan agajin gaggawa da zarar abin ya faru. A garin Majiya ‘yan sanda sun kasa hana jama’a ɗiban mai, duk da cewa sun killace yankin tare da yin gargaɗi, amma yawan jama’a ya cika su. Wannan yana kira da a gayyaci isassun mazaje masu aikin sa-kai, ciki har da ƙungiyoyin ’yan sintiri, a duk lokacin da irin wannan haɗari ya afku.

Kamar yadda rundunar FRSC ta bayar da umarni a kan lamarin Majiya, jami’an da ke kula da tankokin mai ya kamata su tabbatar da cewa dukkan motocin dakon man fetur sun bi ƙa’idojin tsaro kafin su riƙa safarar mai. ƙari ga wannan buƙatu shi ne buƙatar wayar da kan jama’a game da haɗarin wuce gona da iri na direbobi, inda wasu kan shiga gari cikin al’umma motarsu maƙil da mai. Lamarin na Majiya ya faru ne a lokacin da direban mai shekaru 32 ya yi ƙoƙarin kauce wa wata babbar mota a lokacin da yake cikin tsananin gudu, lamarin da ya sa tankar ta fita daga jikin motar. Da ya kasance yana tafiya ne a tsanaki, da hakan bai faru ba.

Dangane da wannan akwai mugun yanayi da hanyoyin Nijeriya ke ciki. Don haka ya kamata gwamnati ta gyara hanyoyin da za a riƙa dakon mai don ceto al’umma daga waɗannan tashe-tashen hankula. Haƙiƙa muna kira ga shugaba Bola Tinubu da ya cika alƙawarin da ya ɗauka, a saaon ta’aziyyarsa ga Majiya, cewa gwamnatinsa tare da haɗin gwiwar jihohi za su tabbatar da yin nazari cikin gaggawa da kuma cikakken nazari kan ƙa’idojin tsaron sufurin man fetur a faɗin ƙasar nan.

By ukarofi