Kwankwaso da Ganduje ku haɗa kan ku don ceto Arewa – Hajiya Binta Hamdan

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

An shawarci jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya, tsohon Ministan Tsaron Nijeriya jagoran siyasar Kano da cewa ya yi haƙuri ya haɗa kai da wanda ya gaje shi a matsayin gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, domin haɗin kan Kwankwaso da Ganduje alkairi ne ga mutunen Kano da ma Arewa baki ɗaya, domin su ceto Arewa da al’ummarta daga ƙangin da Arewa ta faɗa na talauci, fatara, rashin tsaro, lalacewar tarbiyya da sauran matsaloli haɗin kan Ganduje da Kwankwaso zai yi tasiri wajen samar wa Arewa kyakkyawar mafita kamar yadda rabuwarsu ke cutar da Kano da Arewa baki ɗaya, kuma wannan rabuwa babu wanda ta ke amfana sai maƙiya Kano maƙiya Arewa maƙiya Nijeriya domin ci gaban Kano cigaban Arewa, ci gaban Arewa cigaban Nijeriya ne, don haka akwai buƙatar Kwankwaso da Ganduje su haɗa kansu domin ceto Arewa kamar dai yadda Hajiya Binta Abdulwahab, shugabar kamfanin samar da abinci na Hamdan ta bayyana a hirar ta da manema labarai a Kano.

Haka kuma Binta Hamdan ta shawarci tsohon gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje shugaban riƙo na Jam’iyyar APC a halin yanzu da cewa ya fifita ci gaban Kano da Kanawa da ceto rayuwar al’ummar Arewa a kan buƙatun kan sa, ya haɗa kai da tsohon mai gidansa wanda ya yi wa mataimakin gwamna har sau biyu kuma ya gaje shi a matsayin gwamnan Kano a 2015 zuwa 2019 domin ceto Arewa a halin da ta ke ciki, domin magana da murya ɗaya da jiga-jigan Kano, abu ne da zai yi tasiri a siyasar Nijeriya kuma ina jadadda cewa babu masu jin daɗi da rabuwar Kwankwaso da Ganduje sai maƙiya Kano maƙiya Arewa maƙiyan Nijeriya.

A ƙarshe Hajiya Binta Hamdan ta ce, “akwai buƙatar dattawan Kano ‘yan kasuwar Kano, sarakunan Kano, ‘yan siyasar Kano, da ma ɗaukacin su na arewacin Nijeriya, da sauran su su haɗa kan su wajan ceto talakawan Nijeriya daga halin da mu ke ciki na tsanani yadda mutane ke kwana da yunwa wannan abu ne da ya kamata kowa ya yi amfani da damarsa wajen aikata alkairi da zai ci gajiyarsa a nan duniya da gobe kiyama kuma kowannen mu ya sanya tausayi da sanin ya kamata da tsoron Allah a kodayaushe.” 

By ukarofi