Wata kotu ta kori duka ‘yan takarar ciyamomin NNPP a Kano

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Babbar kotun tarayya da ke Kano ta rushe dukkan ‘yan takarar shugabancin ƙananan hukumomi da kansiloli 44 na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a zaɓen ƙananan hukumomi da za a yi a ranar Asabar.

Mai shari’a Simon Amobeda ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a bayan ƙarar da Injiniya Muhammad Babayo da wani ɓangare na NNPP suka shigar kan shugabancin jam’iyyar.

Alƙalin kotun ya umurci hukumar zaɓe ta Jihar Kano (KANSIEC) da ta amince da sabon jerin sunayen ‘yan takarar da ɓangaren shugaban jam’iyyar na jiha da aka amince da shi, Dalhatu Shehu Usman, ya gabatar, bisa tsarin mulkin jam’iyyar.

Mai shari’a Amobeda ya kuma haramta wa KANSIEC sakin rijistar masu kaɗa ƙuri’a ga jam’iyyar NNPP domin gudanar da zaɓen da aka shirya yi a ranar 26 ga Oktoba, 2024. Ya ce KANSIEC ta duba jerin ‘yan takarar da masu ƙarar suka gabatar kawai.

Bugu da kari, kotun ta umarci shugaban ‘yan Sanda na Ƙasa da kuma hukumar DSS da kada su bayar da tsaro a wajen zaɓen ƙarƙashin wannan tsarin.

By ukarofi