NNPC ya fara bai wa matatar Ɗangote ɗanyen mai a Naira

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Matatar man Dangote ta fara dakon ɗanyen mai daga kamfanin mai na ƙasa NNPCL, ƙarƙashin yarjejeniyar sayar da ɗanyen mai a naira, kamar yadda jami’an matatar man da gwamnatin tarayya suka tabbatar a ranar Talata.

An tattaro cewa an fara jigilar ɗanyen man zuwa matatar a cikin makonni uku da suka gabata lokacin da gwamnati ta fara sayar da ɗanyen man ga matatun ƙasar a cikin kuɗin ƙasar.

Wata majiya mai cikakken bayani game da cinikin ɗanyen mai a cikin gida ta shaida wa manema labarai cewa, matatar ta na jiran karɓar ƙarin ɗanyen man fetur daga kamfanin NNPCPL, ƙungiyar da ke kula da albarkatun man ƙasar.

Sun kuma tabbatar da cewa kamfanin da ke Lekki na dalar Amurka biliyan 20 a yanzu an shirya fara sayar sayar da man fetur kai-tseye ga ‘yan kasuwa bayan janyewar dillancin man da babban kamfanin mai na ƙasar NNPCL ya yi.

‘Yan kasuwar da dama – waɗanda suka jima suna shigo da man daga ƙetare – sun zaƙu a fara sayar musu da man kai-tseye daga matatar ba tare da wani mai dillanci a tsakiya ba.

A makonnin da suka gabata ne dai babban kamfanin mai na ƙasar, NNPCL ya sanar da janyewa daga dillancin man na Dangote, domin bai wa ‘yan kasuwar damar sayen man kai-tseye daga matatar.

Ana ganin wannan matakin zai kawo sauƙi ga matsalar ƙarancin man fetur da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar.

By ukarofi