An kwantar da Bobrisky a asibiti

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa fitaccen ɗan daudun nan, Okuneye Idris, wanda aka fi sani da Bobrisky, ya kamu da rashin lafiya yayin da yake tsare a sashin binciken manyan laifuka na rundunar (FCID) Anneɗ, Alagbon, Legas.

Idan ba a manta ba hukumar shige da fice ta Nijeriya NIS ta kama Bobrisky a daren ranar Litinin bayan kama shi a kan iyakar Seme da ke Legas a yayin yunƙurin ficewa daga ƙasar.

Manhaja ta gano cewa bayan da ya kwana tsare a wajen ‘yan sanda, an garzaya da Bobrisky asibitin ‘yan sanda na Falomo domin kula da lafiyarsa.

Wata majiya ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa an ɗauke shi daga FCID zuwa asibiti domin yi masa magani.

Majiyar ta ce, “Bobrisky ya yi ƙorafin ciwon ‘nono’ inda aka garzaya da shi asibitin ‘yan sanda da ke unguwar Falomo a Legas da misalin ƙarfe 2:00 na rana a cikin motar asibiti mai lamba LND 339L. Baƙar riga ya saka, ya rufe fuskarsa da wani ƙyalle, sannan ya kwanta a cikin motar asibiti.”

By ukarofi