Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya naɗa tsohon edita na Blueprint Weekend, Malam Ibraheem Musa, a matsayin babban sakataren watsa labaransa (CPS).
An sanar da naɗin a jiya ta hannun Fabian Anawo, mai ba gwamna shawara kan bincike da dabaru, inda aka bayyana cewa naɗin ya fara aiki nan take.
Malam Ibraheem Musa, gogaggen ɗan jarida ne da ke da fiye da shekaru 30 na ƙwarewa a harkar jarida. Kafin wannan naɗin, ya riƙe muƙamin mai ba gwamna shawara kan harkokin yaɗa labarai.
Ibraheem Musa ya kuma riƙe muƙamai daban-daban a baya, ciki har da edita na farko na Blueprint Weekend, da kuma memba na Kwamitin shirye-shiryen New Nigerian Newspapers. Ya maye gurbin tsohon sakataren watsa labarai na gwamnan, Mohammed Lawal Shehu, wanda aka zaɓa a matsayin Shugaban Ƙaramar hukumar Soba a Kaduna.
