Zaɓen ƙananan hukumomi: NNPP ta lashe duka kujerun ciyamomi da kansiloli a Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

An sanar da jam’iyya mai mulki a Jihar Kano, NNPP a matsayin wacce ta yi nasarar lashe zaɓen duka ciyamomi 44 na ƙananan hukumomin jihar da duka kujerun kansiloli 484 da aka kammala a yau.

Shugaban Hukumar zaɓe ta jihar (KANSIEC), Farfesa Sani Lawal Malumfashi ya sanar da hakan wa manema labarai a hedikwatar KANSIEC a birnin Kano.

Farfesa Malumfashi ya bayyana zaɓen a matsayin wanda aka yi shi cikin lumana wanda ke tattare da gaskiya da adalci inda ya ce babu kujera ɗaya da sauran jam’iyyu 18 da suka fafafa suka samu.

Duk da yunƙurin dakatar da gudanar da zaɓen da wasu jam’iyyu suka yi gabannin aiwatar da shi, Babbar Kotun jihar, ta bai wa KANSIEC izinin yin sa a lokacin da aka tsara shi.

Mai Shari’a, Sanusi Ma’aji, shi ya yi hukunci game da ƙarar da KANSIEC ta shigar akan jam’iyyar APC da wasu 13 da suka nemi a dakatar da gudanar da zaɓen a lokacin da aka tsara.

By Babaji