
Daga BELLO A. BABAJI
Kimanin mutane 40 ne ruftawar wani gini ya rutsa da su a yankin Sabon Lugbe da ke Abuja.
Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar.
A halin yanzu al’umma na cike da alhini game da iftila’in yayin da jami’an gaggawa suka garzaya wajen da abin ya faru don bada agaji ga mutane da dukiyoyinsu.
Sauran bayani zai I daga baya.