
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙasar Birtaniya ta bai wa sojojin Nijeriya kyautar kayan aiki na zamani da adadinsu ya kai Naira biliyan ɗaya don ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin rundunar sojin ƙasar da na Nijeriya.
Cikin wani saƙo da Babbar Hukumar Birtaniya ta fitar a Abuja ranar Juma’a, ta ce tallafin kayan aikin zai tai wa yaƙin da sojojin su ke yi da ƴan ta’adda a yankin Arewa-maso-Gabashin Nijeriya.
Haka kuma an bada tallafin ne a lokacin da wasu daga cikin sojojin Birtaniya ke gudana da wani karatu da musamman kan ƙwarewa a aikin soja waɗanda a halin yanzu su ke Maiduguri.
Shugaban jami’an haɗaka na Arewa ta Gabas (JTF NE), Manjo-Janar Wahidi Shua’ibu shi ya karɓi tallafin a Maiduguri.
