Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kimanin ƙananan Hukumomi 352 a jihohi 17 da Babban Birnin Tarayya sun gaza samun ko Kobo a matsayin kuɗaɗen shiga cikin asusun gwamnatocin jihohinsu a shekarar 2023, kamar yadda bayanai daga Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) suka nuna.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fafutuka na bai wa ƙananan Hukumomi ’yancin cin gashin kansu.
Wani bincike da aka yi daga asusun tattara kuɗaɗen shiga na cikin gida da NBS ta buga kwanan nan ya nuna cewa adadin ya samu aarin jihohi 10 ne daga jihohi bakwai da ba su fitar da kudaden shiga ko samar da kudaden shiga a shekarar 2022 ba.
Hukumar ƙididdiga a cikin rahoton ta ce, cikin jihohi 36 na Nijeriya 20 ne kawai suka samu kudaden shiga daga ƙananan hukumominsu a shekarar 2023.
Wannan lamarin ya ƙara jaddada ƙalubalen kuɗi da ya dabaibaye ƙananan hukumomi tare da sanya ayar tambaya game da yadda ake tafiyar da albarkatun ƙasa yadda ya kamata a matakin ƙananan hukumomi, musamman a irin yanayin da ake ciki na neman ‘yancin cin gashin kai da riƙon amana a bangaren.
A watan Mayu, gwamnatin tarayya, wanda babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi ya wakilta, ta shigar da ƙara domin ƙalubalantar ikon da gwamnonin ke da su na karɓa da kuma hana kudaden da gwamnatin tarayya ke bai wa ƙananan hukumomi.
Kotun ƙoli, a ranar 11 ga Yuli, 2024, ta ba da wani muhimmin hukunci da ke tabbatar da cin gashin kai na harkokin kuɗi na ƙananan hukumomi 774 na ƙasar tare da yanke hukuncin cewa gwamnoni ba za su iya sarrafa kuɗaɗen da aka ware wa ƙananan hukumomin ba
