Zargin rashin lasisi: Ƙungiyar NBMOA ta maka Arewa24 a kotu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kwamitin Amintattu na ƙungiyar Masu Gidajen Yaɗa Labarai na Arewa, NBMOA, ya shigar da ƙara a kan kamfanin yaɗa labarai na Arewa 24 da wasu kamfanoni bakwai, inda ya zarge su da gudanar da ayyukansu ba tare da cikakken lasisi ba.

Babbar kotun tarayya da ke Abuja za ta saurari ƙarar, ƙarƙashin mai shari’a Omotosho.

Kotun ta bayyana sunayen Hukumar Kula da Watsa Labarai ta ƙasa (NBC), Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a ta Tarayya, Hukumar Kula da Tallace-tallace ta Nijeriya (ARCON), Hukumar Kula da Gasa a Tsakanin Kamfanoni (FCCPC), ƙungiyar Ma’aikata Masu Zaman Kanta ta Kafafen Yaɗa Labarai (MIPAN), da kamfanonin talabajin na MultiChoice, StarTimes, da ƙungiyar Masu Talla ta Nijeriya (ADɓAN) a matsayin waɗanda ake tuhuma.

A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar NBMOA Alhaji (Dr.) Ahmed Tijjani Ramalan ya fitar a Abuja, ya bayyana damuwarsa kan yadda ake zargin waɗanda ake tuhuman na ayyukan da ba a ba su izini ba, na lalata tsarin kafafen yaɗa labarai na Njjeriya, wanda zai iya yin illa ga masu gidajen jaridu da jama’a.

“Manufarmu ita ce tabbatar da adalci, ingantaccen yanayin watsa labarai daidai da kafaffen ƙa’idojin watsa shirye-shirye, tare da ci gaba da sadaukar da kai ga bin doka,” in ji Ramalan.

Hukumar ta NBMOA ta sake nanata sadaukarwar ta ga ƙa’idojin watsa shirye-shiryen da suka dace kuma ta bayyana cewa ba za ta sake yin tsokaci ga jama’a ba har sai an kammala tsarin shari’a, don mutunta tsarin shari’a.

Masu ruwa da tsaki a masana’antu na sa ido sosai kan wannan lamari, wanda zai iya yin tasiri mai yawa ga ƙa’idojin watsa labarai da kuma ƙa’idojin lasisi a faɗin Nijeriya.

By ukarofi