
Daga BELLO A. BABAJI
Kwamandan Sojojin Amurka na reshen Nahiyar Afirka (AFRICOM), Janar Michael Langley ya ziyarci Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa a Hedikwatar Tsaro dake Abuja, inda ya yaba wa ƙasar bisa tsarinta na ƙoƙarin daƙile matsalolin rashin tsaro.
Darkatan Labaran sojojin Nijeriya, Burgediya Janar Tukur Gusau ya ce, Janar Langley ya taya Janar Musa bisa naɗa shi Shugaban kwamitin ƙasashen ECOWAS na jagororin tsaro, ya na mai amincewa da ƙwarewarsa ta shugabanci.
Ya ce haɗin kai da horo na sojojin Amurka da na Nijeriya za su taimaka wajen daƙile ayyukan ta’addanci da ke addabar yankin Afirka ta Yamma.
A nasa jawabin, Janar Musa ya yi godiya ga ba’amurken sojan bisa ziyarar tasa, ya na mai tabbatar masa da cewa sojojin Nijeriya a shirye su ke su bada haɗin kai ga sauran ƙasashe don ganin an magance matsalolin tsaro a shiyyar.
Ya kuma nemi a ƙarfafa alaƙar harkokin tsaro na ɓangarorin biyu ta fuskokin horo, raba bayanan sirri da kuma mallakar duk wani abin da zai taimaka wa harkar tsaro.
Ziyarar kwamandan ta nuna muhimmancin inganta alaƙa tsakanin Nijeriya da Amurka musamman ga daƙile matsalolin taɓarɓarewar tsaro a shiyyar.
