Wani ɗan ƙasar Amurka, Anthony Nephew, ya harbe kansa, matarsa, tsohon abokin aikinsa, da kuma ‘ya’yansa biyu bayan zaɓen da aka yi a ranar 5 ga watan Nuwamba wanda ya kawo zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Donald Trump kan karagar mulki.
A cewar hukumomin da suka yi magana da jaridar New York Post ranar Lahadi, mutumin mai kimanin shekaru 46, ɗan Minnesota ya matuƙar nuna fushinsa kan zaɓen Trump da aka yi a matsayin shugaban ƙasa.
“Wanda ya yi harbin, yana ɗauke da “lalurar rashin lafiyar ƙwaƙwalwa,” inji shugaban ‘yan sandan Duluth Mike Ceynowa a ranar Juma’a, kwana guda bayan da hukumomi suka gano gawarwakin mutane biyar a cikin gidaje biyu a cikin birnin.
Hukumomi sun gano tsohon abokin aikin Anthony Nephew, Erin Abramson, mai shekaru 47, da ɗansu, Jacob Nephew, mai shekaru 15, kwance a gidansu, inda suka haɗu da ajalinsu sakamakon harbin bindiga da aka yi a gidansu da yammacin ranar Alhamis, inji ‘yan sanda.
Bayan bayyana Anthony Nephew a matsayin wanda ake zargi, ‘yan sanda sun gano matarsa mai shekaru 45, Kathryn Nephew, da ɗansu Oliɓer Nephew mai shekaru 7 a duniya, sun mutu sakamakon harbin bindiga a gidansu da ke kusa.
Kafin wannan bala’in, Anthony Nephew ya kasance yana yaɗa munana maganganu, da kuma na nuna ƙin jinin Trump a shafinsa na Facebook.
“Lafiyar ƙwaƙwalwata da kuma tafiyar duniya ba za su iya zama tare cikin lumana ba, kuma yawancin dalilan dai addini ne,” Anthony Nephew ya wallafa a watan Yuli.
A wata wallafar Kathryn cewa ya yi, “Na tsorata da masu kishin addini da suke nuna mummunar aƙidarsu a kaina da iyalina, wanda ya kai ni ga tunanin yuwar kona ni bayan an ɗaure ni akan icce a matsayin maye ko kuma a gicciye ni a kan gungumen azaba.
“Samun mutane a zahiri da suka gaskata cewa ni ko ɗana Shaidan ne, ko mun kasance maƙiyan Yesu, ko duk wani abu da suka fi so da tsoro a wannan makon.”
A wani saƙon kuma, ya zargi ‘yan jam’iyyar Republican da “wahalar da mata” tare da cin zarafin su.
“Gilead ga mu mun zo,” ya rubuta, yana mai nuni ga The Handmaid’s Tale, wani littafi na dystopian da aka juya zuwa fim mai dogon zango, mai suna ‘Hulu’, wanda ke nuni da tauye haƙƙin mata, tare da tilasta musu haihuwa ga masu mulki.
Anthony Nephew ya kuma wallafa wasu ‘yan siyasa, ciki har da hoton tsohon shugaban ƙasa Barack Obama, Trump, Shugaba Joe Biden, da mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris. A ƙarƙashin hoton Trump ya rubuta ƙalmar “ƙiyayya” yayin da kalmomin “fata,” “warkarwa,” da “girma” suke ƙarkashin sauran ‘yan siyasar da ya wallafa waɗanda ke ƙarƙashin inwar Jam’iyyar Democrat.
“Ba wai kowa ya damu ba, amma a matsayina na mai jefa ƙuri’a mai zaman kansa, ina matuƙar son ganin jam’iyyun siyasa a ƙasarmu biyu sun zaɓi ‘yan takara mafi inganci,” inji shi a watan Yuli.
A baya, Anthony Nephew ya ba da gargaɗi mai ban tsoro game da gwagwarmayar sa da lafiyar ƙwaƙwalwa, yayin da ya yi rubutu a cikin Duluth News Tribune a cikin 2021, inda yake cewa, “Ga miliyoyin Amurkawa, matsalar ƙwaƙwalwa na haifar da kashe kanka, ko kashe wasu kafin kashe kanka.”
“Ana ƙyamatar masu matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa a ƙasar nan, ana yin watsi da su, ko kuma a ɗauke su a matsayin wani nauyi da mutum zai ɗauka shi kaɗai, ga uwa uba rashin fahimta,” ya rubuta.
“Amurkawa sun musanta cewa, suna fama da matsalar taɓin hankali saboda dole su yi hakan, ko saboda an gaya musu hakan, ko kuma saboda ba su gane cewa hankalinsu ya samu rauni ba,” ya ƙara.
‘Yan sanda a Duluth, wani birni mai kusan mutane 90,000 da ke da nisan mil 135 daga Arewacin Minneapolis, har yanzu ba su tantance dalilin yin harbin ba.
