Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Wani malamin addinin Kirista mai suna Rabaran Moses Sunday mai ritaya ne ya yi kiran a wa’azinsa a wajen sujadar Lahadi na Cocin ECWA 3 dake Tudun-gwandara a Lafiya babbar birnin jihar Nasarawa.
Ya ce ba shakka kiran ya zama wajibi idan aka yi la’akari da yadda rayuwar handama ya zama ruwan dare a rayuwar al’umma yanzu ciki har da mabiya Kiristoci.
Rabaran Moses Sunday ya bayyana cewa a yanzu da zarar mutum ya mutu sai a riƙa tunanin handame dukiyoyin sa ba tare da tausaya wa ‘ya’ya da matan da ya bari a raye ba batare kuma da tsaron Allah ba.
Ya ba ba misali da wani mutum da ɗan uwansa ya rasu inda nantake sai ya zo yana sanar wa jama’a cewa a lokacin da ƙan uwan nasa ke raye ya gaya masa cewa idan ya mutu ka da a binne gawarsa a filin saba a kai ƙauye inda daga bisani bayan an bincika sai aka gano ba gaskiya ba ne.
Malamin addinin Kirista ɗin Rabaran Moses Sunday ya kuma bayyana cewa hanyoyin handama sun haɗa da ƙwace dukiyar da ba na mutum ba da handamar abinci kamar yadda mata ke yi a gidan biki da zamba cikin aminci da shaidar zu da dai sauran su inda ya gargadi mabiya kiristoci da sauran al’umma baki daya su guji hakan kafin su fuskanci fushin Ubangiji maimakon haka acewarsa dole ne a rika yin rayuwa irin ta Isah Almasihu na kauna da tausayawa al’umma musamman talakawa da wadanda suka rasa mazajensu da marayu da sauran su don akarshe a samu ra’amar Allah.
Sauran abubuwa da aka gudanar a yayin sujadar Lahadin na Cocin ECWA 3 na Tudun-gwandaran sun haɗa da rewa waƙoƙin yabon Ubangiji na musamman daga ƙungiyoyin cocin daban-daban da gudanar da addu’o’i na musamman don zaman lafiyar ƙasar nan da samun sauƙin marasa lafiya da dai sauransu.
