Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta tabbatar da kawo ƙarshen ƙungiyar yan ta’adda da ake kira ‘Lukarawa’ a shiyyar Arewa maso yammacin nan ba da jimawa ba.
Ribadu ya bayyana haka ne a lokacin da ya wakilci shugaban ƙasa Tinubu a wajen bikin buɗe babban taron kwastam na shekarar 2024, ranar Laraba, a Abuja.
“Za mu fatattaki waɗanda ake kira Lukarawa daga ƙasarmu. Za mu kunyata masu sukar mu kuma zamu rufe bakunansu. Boko Haram da suka addabi ƙasarmu a baya, yanzu tserewa suke. Yanzu haka mambobinta suna tafiya zuwa wasu kasashe makwabta saboda basu da damar yin ta’addancin su a Nijeriya” inji shi.
Ya kuma bayyana cewa, alamun na ƙara nuna cewa al’amura na cigana da inganta ta fuskar tattalin arziki a ƙasar nan wanda kowa zai iya gani, inda ya ba da misali da yadda ake hako ɗanyen mai a yankin Neja-Delta da kuma sauye-sauyen kasafin kudi da babban bankin Nijeriya (CBN) ke yi a cikin irin wannan ƙoƙari.
“Haƙar ɗanyen mai ya kai ganga miliyan 1.8 a kowacce rana. sannan kuma an tsaftace babban bankin ƙasa; babu wanda ke ɗaukar kobo daga babban bankin. Mun yi alƙawarin cewa za mu gyara ƙasar nan, kuma za mu yi hakan domin Shugaba Tinubu bai taɓa zama mutum mai gazawa ba,” inji shi.
