An dakatar da Mourinho tare da cin sa tara

Spread the love

An dakatar da Jose Mourinho wasa ɗaya da cin sa tarar Yuro 15,000 sakamakon caccakar alƙalan wasa a karawar da Fenerbahce ta doke Trabzonspor.

Tsohon kocin Chelsea da Manchester United ya shiga fili a guje da faɗuwa ƙasa da gwiwa biyu, bayan da Sofyan Amrabat ya ci ƙwallo na uku daf a tashi.

To, sai dai kocin ya soki alƙalan wasan babbar gasar tamaula ta Turkiya kan yadda suke gabatar da aikinsu.

Hukumar ƙwallon ƙafar Turkiya ta ce, kalaman da Mourinho ya yi ba su kamata ba kuma sun saɓa ƙa’ida.

Ta ƙara da cewa, tsohon wanda ya horar da Real Madrid da Inter Milan ya yi furucin da zai ɓata ƙwazon alƙalan da sauran jami’ai kan batun son rai da rashin adalci.

Wasan da ya ci karo da taƙaddama, Mourinho bai ji daɗin da aka bai wa mai masaukin baƙi Trabzonspor fenariti biyu ba, waɗanda dukkansu sai da aka tuntuɓi ɓAR, wadda ta fayyace abinda ya faru.

Ya kuma ce su kansu ya kamata a ba su bugun fenariti tun kan su ci ƙwallo na uku ta hannun Amrabat.

By ukarofi