Tirela ɗauke da gas ta kama da wuta a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Wata motar tirela ɗauke da man gas ta kama da wuta a daidai gidan man Tamal dake yankin Magama a hanyar ƙaramar hukumar Jibiya a ranar Alhamis.

Wannan al’amari ya jefa al’ummar garin Magama da Jibiya cikin fargaba da tashin hankali.

Motoci 6 ne suka ƙone ƙurmus a inda kuma ba a rasa rai ko ɗaya ba.

Jami’an tsaro na ƴan sanda da sojoji suka kai ɗauki na gaggawa har inda suka samu nasarar kashe wutar.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar ƴan sandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya bayyana cewa, tuni kwamishinan ƴan sanda, CP Aliyu Abubakar Musa ya bada umurnin binciken musabbabin gobarar.

By Babaji