
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
An bai wa al’ummar ƙaramar hukumar Gaya ta Jihar Kano tabbacin inganta harkar lafiya a yankin yadda ya kamata saboda muhimmancinta ga rayukan al’umma.
Zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar, Mahmud Tajo Gaya ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa ta musamman da Sashin Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Lafiya, karkashin jarorancin Ibrahim Abdullahi, a lokacin da tawagar duba aikin rigakafin shan-inna da aka kammala kwanan nan ta ziyarci yankin, inda aka tattauna a ofishin Shirin Rigakafi na Ƙasa (NPI) reshen yankin.
Tajo Gaya ya ce yana da sha’awa game da harkar lafiya kasancewar tun asali shi ma’aikacin lafiya ne, kuma tsohon Mai Taimaka wa Gwamna na Musamman akan Asibitin tafi da Gidanka da ake duba mutane a faɗin jihar Kano da ba su magani kyauta musamman a wurare masu nisa da wahalar shiga.
Ya ce ya tsotsi sha’awar inganta lafiya ne daga wajen Gwamna jihar, Abba Kabir Yusuf, da Kwamishinan Lafiya, Dakta Abubakar Labaran Yusuf wanda bayan an zaɓe shi ne ya ƙudiri aniyar inganta fannin a ƙaramar hukumar ta hanyar bijiro da hanyoyi daban-daban domin sauƙaƙa wa al’ummarsa.
“Tun da na shiga ofis ban huta ba. Na ziyarci cibiyoyin lafiya na yankin don ganin yadda abubuwa ke tafiya. Nan da nan na bada umarnin ɗaga likkafar asibitoci biyar su rinƙa yin aiki cikin awanni 24. Zan cigaba da tallafa wa duk wani shiri da zai taimaki al’ummarmu. Babban abin da na sa a gaba shi ne, inganta lafiya, lafiya, lafiya”, inji Tajo.
“Lokacin na na zo na tarar akwai cutar kwalara nan da can a wasu sassa na ƙaramar hukumar da ta shafi kimanin mutane hamsin kwance a asibitoci. Mun kula da su har aka sallame su, sannan na bai wa kowanne daga cikinsu N10,000.”
Shugaban ƙaramar hukumar ya ce yana shirin inganta ƙwarewa da ilimin ma’aikatan lafiya domin a ƙara musu karsashi ta yadda za su yi abin da ya kamata, ya ƙara da cewa abin da yake so daga gare su shi ne su zama masu gaskiya da riƙon amana yayin gudanar da aikinsu domin a inganta tsarin lafiya a ƙaramar hukumar.
Kazalika, ya nuna gamsuwa da yadda ya samu sashin da sadaukarwar da ma’aikatan lafiya ke nunawa yayin da suke gudanar da ayyukansu a cibiyoyin lafiya inda ya hore su da su riɓanya ƙoƙari don al’ummarsu.
Sannan kuma yi godiya ga al’ummar ƙaramar hukumar bisa goyon bayan da suke ba shi tun lokacin da ya zo tare da yin kira gare su da su cigaba da mara wa manufofi da tsare-tsaren da ya zo da su na ciyar da karamar hukumar gaba baya, ya na mai tabbatar musu da shimfiɗa ingantaccen shugabanci.
