Hukumar zaɓe za ta fara tantance ƴan takarar ciyamomi da kansiloli a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar Katsina, ta ce za ta fara tantance ƴan takarar kujerun ciyamomi da kansiloli na ƙananan hukumomi a mako mai zuwa.

A wata takarda da ke ɗauke da sa hannun Alhaji Adamu Salisu Ladan, kwamishinan zaɓe, ya ayyana 20 zuwa 27 na wannan wata a matsayin ranakun da hukumar za ta tantance ƴan takarar.

Ya bayyana cewa za a tantance ƴan takarar kujerar ciyaman a ofishin hukumar yayin da na kansiloli kuma za a yi su a sakatariya ta kowacce ƙaramar hukuma da suka fito.

Kwamishinan ya shawarci ƴan takarar su tabbatar sun shirya takardun da hukumar za ta buƙata kafin fara aikin tantacewar.

Ya kuma ya gargaɗin cewa kowane ɗan takara jam’iyyarsa ce kawai za ta ɗauki nauyin shigarsa zaɓe, kuma hukumar ba zata ƙara ko kwana guda ba na aikin tantacewar.

Ana sa ran ranar 15th ga watan Fabrairun shekara mai zuwa hukumar zaɓen za ta gudanar da zaɓen kananan hukumomin jihar.

By Babaji