
Daga BELLO A. BABAJI
Majalisar Kula da Alƙalai ƙarƙashin jagorancin Allƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta hukunta wasu alƙalai biyar bisa laifin rashin kiyaye ƙa’idodin aiki.
A yayin zamanta na ranar Alhamis, majalisar ta dakatar da Mai Shari’a G. C. Aguma na Babbar Kotun Tarayya dake Jihar Ribas kan gudanar da ayyukan shari’a na shekara ɗaya ba tare da biya ba sannan da sanya shi a sahun waɗanda za ake sa wa ido na tsawon shekaru biyu.
Haka ma an dakatar da Mai Shari’a A. O. Nwabunike na Babbar Kotun Tarayya dake Jihar Anambara bisa irin laifin da na farkon ya aikata da kuma sanya shi a sahun waɗanda ake sa wa ido.
Haka kuma, majalisar ta nemi a yi wa Alƙalan kotuna biyu ritayar dole bisa laifin ƙaryar shekaru. Alƙalan sune Mai Shari’a T. E. Chukwuemeka Chikeka na Jihar Imo da kuma Ƙadi na Jihar Yobe, Babagana Mahdi.
Bugu da ƙari, majalisar ta samar da kwamitoci guda shida don cigaba da bincike game da ƙararraki 30 da aka shigar duk da ta yi watsi da wasu 22 saboda rashin nagarta.
Har’ilayau, majalisar ta naɗa kwamitin da zai yi bincike game da baki ɗaya ƙararrakin da aka shigar kan Mai Shari’a O. A. Ojo, Alkalin Alƙalan Jihar Osun.
