



Daga BELLO A. BABAJI
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya jaddada goyon bayan Gwamnatin Tarayya kan bikin girmama wa ta Oscar da za a sanya Dala miliyan 618 a shirin Digital da kasuwancin zamani (iDICE), yayin da Nijeriya ta zaɓi fim ɗin Mai Martaba ya lashe lambar yabon.
Shettima ya ce musamman waɗanda suka shirya shi za su samu aikin iDICE da zai inganta harkokin Digital da masana’antu masu ƙirƙira.
A lokacin da ya ke jawabi a wani zama da tawagar da suka haɗa fim ɗin ƙarƙashin jagorancin Ministar Al’adu, Barista Hannatu Musawa a Fadar shugaban ƙasa, Shettima ya bayyana farin cikinsa tare da alfaharin kasancewar sa ɗan Nijeriya.
Ya ce za su tabbatar da tafiya tare da duk waɗanda suka taimaka wajen ɗaga darajar Nijeriya, ya na mai nuna muhimmancin haɗin kan ƴan ƙasa ta masana’antar finafinai.
Ya kuma yi kira ga Ministar da ta jagoranci yaƙin neman amincewar kowane ɓangare don Nijeriya ta yi nasara a Oscars.
Fim ɗin ‘Mai Martaba’ da Prince Daniel ya bada umarni, ya kasance ɗaya daga cikin finafinan da aka zaɓa kuma ake sa rana zai lashe kyautar gwarzon fim na 2025 a mataki na ƙasa-da-ƙasa.
Minista Musawa ta ce tuni masu zuba hannun-jari suka bada himma wajen gina masana’anta ta zamani da ke aiki bisa hazaƙa da fitar da sababbin abubuwa.
