Hawaye sun bayyana sosai a ranar Juma’a yayin da aka yi jana’izar marigayi Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja a Abuja, inda aka kawo ƙarshen Kyawawan ayyukansa na soja wanda ya shafe shekaru masu yawa a ciki.
An yi jana’izar ne a maƙabartar Ƙasa dake babban birnin tarayya, inda aka kammala kwanaki biyu na jerin abubuwan girmamawa da aka fara a Legas a farkon mako.
An binne shi daidai ƙarfe 4:41 na yamma bayan taron ya dauki tsawon sa’o’i biyu da rabi. Makarar gawar Lagbaja mai launin tutar Najeriya, kore da fari, ta iso maƙabarta da misalin ƙarfe 3:00 na rana a cikin wata motar jana’iza mai launi fari, bayan wani taron addini da aka gudanar a babban cibiyar Kiristoci ta Ƙasa da ke Abuja.
Manyan baƙi da dama sun halarci bikin. Shugaba Bola Tinubu, mataimakin shugaban Ƙasa Kashim Shettima, muƙaddashin babban hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, Babban hafsan tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa, ministan tsaro Abubakar Badaru da sauran manyan jami’an gwamnati da sojoji sun kasance a wajen taron.
A cikin jawabinsa, Shugaba Tinubu ya bayyana naɗin da aka yiwa marigayi Lagbaja a matsayin ɗaya daga cikin kyawawan naɗi da ya taɓa yi tun lokacin da ya hau mulki a matsayin shugaban Nijeriya.
“A matsayin alamar godiyarmu ta har abada, na bai wa marigayi Babban Hafsan Sojojin Ƙasa lambar yabo ta girmamawa na kasa ta CFR (Commander of the Federal Republic),” inji Tinubu, inda ya buƙaci sojoji da kada su rage ƙwazo da mutuwar Lagbaja.
Babban Hafsan Tsaro, Janar Musa, ya ce mutuwar COAS ba za ta rage karfin gwiwar sojoji ba wajen yaƙi da rashin tsaro. Ya ce, “Ga sauran sojoji, mu yi amfani da wannan lokaci don sadaukar da kanmu ga abinda Janar Lagbaja ya tsaya kai.”
