Uwargidan Gwamnan Zamfara ta ƙaddamar da shirin biyan bashi ga mutane 1,000

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau 

Matar gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal, Hajiya Hurriyya ta ƙaddamar da shirin biyan basussuka ga mutane akalla dubu ɗaya a faɗin masarautun jihar 19.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mataimakiya a fannin yaɗa labarai, ta matar Gwamnan, Hajiya Zara’u Musa da aka raba wa manema labarai a Gusau ranar Laraba.

Sanarwar ta ce, an gudanar da wannan sabon tsarin ne a hukumar tattarawa da rabon zakka da waƙafi dake Gusau Babban Birnin jihar.

Uwargidan gwamnan ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne da nufin haɗa kan iyalan waɗanda ke gidan yari, da dawo da martaba da kuma bai wa ɗaiɗaikun mutane damar dogaro da kai.

Uwargidan Gwamnan ta bayyana cewa Gwamna Dauda Lawal ya umurci Hukumar Zakka da Waƙafi da ta shiga tsakani wajen sasanta basussukan a tsakanin al’umma da kuma wasan da aka garkame a gidan gyaran hali saboda rashin iya biyan basussukan dake kansu.

Ta kuma jaddada cewa an kafa wani kwamiti a ƙarƙashin jagorancin alkalin alkalai watau Grand Khadi, tare da Kwanturolan gidan yari da Malamai waɗanda aka ɗora wa alhakin daidaita basussuka da kuma taimakawa wajen gyara auren daya lalace.

“Ina sanar da al’ummar jiharmu cewa, Gwamnan Jihar Zamfara, yana kokarin ganin ya ragewa marasa galihu raɗaɗin talauci da suke ciki a faɗin jihar,” Huriyya ta ce.

Ta kuma bada tabbacin cewa shirin zai ɗore domin ci gaban al’ummar jihar.

By ukarofi