Gwamnatin Zamfara ta gano likitocin bogi 20

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce ta gano likitoci ashirin a ɗaya daga cikin asibitin ta a matsayin likitoci kuma ma’aikatan bogi waɗanda ke karɓar albashin sama da Naira miliyan shida duk wata. 

Shugaban ma’aikata na jiha kuma shugaban kwamitin gudanarwa na kwamitin tantancewa ma’aikata, Barista Ahmed Liman ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Gusau ranar Laraba. 

A cewarsa, gwamnan jihar Dauda Lawal ne ya kafa kwamitin domin tantance ainihin ma’aikatan jihar don aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N70,000. 

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Zamfara tana da ma’aikata sama da dubu talatin da huɗu 34,000 a cikin albashin jihar. 

“Abin takaici ne yadda kwamitin ya gano wasu daga cikin ma’aikatan suna karbar albashi sai biyu yayinda muka gano a asibiti daya mallakin gwamnatin Jihar mun gano cewa yana da likitoci 22 amma biyu ne kawai na gaskiya, yayin da sauran ashirin bamu san inda suke ba, amma suna karɓar sama da Naira miliyan shida duk wata a matsayin albashi,” ya ce.

Barista Ahmed Liman ya bayyana cewa har yanzu ana kan tantancewar, yana mai cewa kwamitin zai kammala aikin nan da ƙarshen wannan wata. 

“Muna yin duk abin da za mu iya don kammala ayyukan mu kamar yadda aka tsara kuma za mu tabbatar da taka tsantsan, gaskiya da adalci a cikin aikin da aka ba mu,” ya ƙara da cewa. 

A cewarsa, irin wannan kwamitin tantancewa gwamnatin jihar ta kafa a dukkan ƙananan hukumomi 14 domin tantance ma’aikatan ƙananan hukumomin domin aiwatar da cikakken mafi ƙarancin albashi na N70,000. 

Ya kuma buƙaci ma’aikatan gwamnati da na ƙananan hukumomi da su ba kwamitin haɗin kai domin samun nasara a aikin tantancewar da ake yi. 

By ukarofi