Dalilinmu na bin diddigin kadarorin masu laifi lokacin bincike – EFCC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban hukumar yaƙi da masu cin dunduniyar tattalin arziƙin Nijeriya, EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa ƙwace kadara a matsayin wani ginshiƙi na yaƙi da laifukan da suka shafi cin hanci da cin dunduniyar tattalin arziƙi kuma wata dabara ta daban.

Olukoyede ya bayyana hakan ne a lokacin da kwamitin majalisar wakilai mai kula da laifukan cin hanci ta ziyarce shi a ranar Taka a Abuja.

“Duk wanda ya fahimci cukumurɗan da ke aikin binciken laifukan da suka shafi kuɗi, zai a fahimci bincike Naira biliyan ɗaya ba ƙaramin yaƙi ba ne,” in ji Olukoyede.

“Don haka na sanar wa da mutane ne cewa da zarar mun fara bincike, to akwai buƙatar mu haɗa da bindiddigin kadarori saboda ginshiƙi ne wajen yaƙi da rashawa,” Olukoyede ya faɗa.

Ya ce idan ka bar masu almundahana suka kai ga bayanan farko da kake tattarawa, to za su yaƙe ka.”

Ya ce da zarar sun fara bincike to sukan kuma fara bin diddigin kadarori inda hakan ya taimaka musu wajen bankaɗo abubuwa masu yawa.

Ya ce manufar kafa hukumar ita ce ciyar da Nijeriya gaba.

Daga nan ne ya gode wa dukkan ma’aikata da jagororin hukumar inda ya bayyana cewa a watan Oktobar 2023, da watan Oktobar shekarar nan, mun yi nasarar kama Naira biliyan 250 da sauran miliyoyin Daloli da miliyoyin kuɗin fa da sauransu.

Sannan ya ce hukumar ta samar da sashen kula da waɗanda ake zargi, wanda haka ya sa suka kai ga miƙa mutane 3,500 daga 28 ga watan Oktobar 2023 zuwa 18 ga watan Oktobar 2024.

Daga nan ya tunawa al’umma illar da ‘yan yahoo-yahoo suke yi wa tattalin arziƙi inda Nijeriya ke kai wa ga rasa Dala 500,000 a kowacce shekara. “Wannan ne abin da mutane suke ɗaukar da wasa.

“Amma duk wannan abu ne da muka san zai faru domin idan kana yaƙar cin hanci to shi ma ƙoƙari yake ya yake ka.”

Olukoyede ya ce baya ga waɗanda suka samu da laifin da aka yi wa hukuncin, akwai shari’o’i da ke gaban kotu.

A cikin shekara ɗaya mun samu ƙorafe-ƙorafe sama da 17,000 inda a yanzu muke kan bincike sama da 20,000 daga watan Oktobar 2023 zuwa yau. Sannan mun buɗe sabbin tuhume-tuhumen 4800.

Shugaban kwamitin yaƙi da cin hanci da rashawa na majalisar wakilai, Ginger Onwusibe, ya ce sun yaba da yadda hukumar ta tafi da kasafinta da lura da abin da ka-je-ya-zo.

Daga nan ne ya ba wa hukumar tabbacin za su ƙara musu yawan abin da ake ba su a cikin kasafin kuɗi na 2025 domin ba su damar cigaba da samun nasara a aikinsu.

Ya kuma ce shugaban hukumar ya nuna jarumta wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar nan ba tare da kallon wane ɗan wane ne ba ko kallon addini ko ƙabila ba a yayin aikinsa.

By ukarofi