Ɗangote ya fi kowa kyautata biyan haraji a Nijeriya – FIRS

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An karrama rukunin Ɗangote da sauran rassansa da lambar yabo ta FMDƙ mai zinare a matsayin kamfanin da ya fi biyan haraji a Nijeriya.

Kamfanin Ɗangote Industries Limited (DIL) da Bluestar Shipping, wani reshensa, an san su ne a matsayin waɗanda suka fi biyan haraji a ƙasar nan gabanin kamfanin sadarwa na MTN, yayin da babban kamfanin ƙera siminti na ƙasar, Dangote a wani lokaci ya samu lambobin yabo uku a na FMDQ.

An gudanar da taron miƙa lambar yabon ne a Legas.

A yayin bikin ranar musamman ta Hukumar Tara Haraji ta ƙasa, FIRS, a wajen bikin baje kolin kasuwanci na ƙasa da ƙasa da aka kammala a Legas, hukumomin kula da haraji na ƙasar sun bayyana Dangote a matsayin wanda ya fi biyan haraji a Nijeriya.

By ukarofi