
Daga BELLO A BABAJI
Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana abin da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ke yi a matsayin barazana ga demokraɗiyya, ya na mai kira ga Shugaba Tinubu da ya ɗauki mataki akansa.
Cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun kakakinsa, Olawale Rasheed, Adeleke ya bayyana hakan ne a lokacin da Ganduje ya ce zai ƙwace Osun a zaɓen 2026 bayan nasarar da APC ta samu a zaɓen gwamnan Ondo a kwanan nan.
Gwamna Adeleke ya zargin Ganduje da haifar da tsaiko ga zaman lafiya da haɗin kan al’ummar Kudu-maso-Yamma da kuma ƙoƙarin sauya matsayar Shugaba Tinubu na yin zaɓen 2027 cikin lumana.
Ya kuma bayyana kalaman Ganduje a matsayin adawa da demokraɗiyya da nakasa martabar Tinubu game da sha’anin demokraɗiyya.
Ya ƙara da cewa, kasancewar jam’iyyar ta yi nasara a Edo da Ondo ba shi ke nuna haka ne zai faru a Osun ba saboda dalilai na cikin gida.
Har’ilayau, ya bada misali da Kano a inda ya ce duk da Ganduje ya shekara takwas da kujerar mulkin jihar, amma tafiyar Kwankwasiyya ke jagorantcin siyaysarsu.
