Matatar man Ɗangote ta fara safarar mai zuwa ƙasashen Afirka ta Yamma

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Matatar man fetur ta Ɗangote ta fara fitar da mai da aka tace zuwa ƙasashen yammacin Afirka, abin da ke nuna yiwuwar wannan matata za ta girgiza kasuwar mai a yankin. Rahoton Bloomberg a ranar Talata ya tabbatar da hakan, inda ya ambaci bayanai daga Vortexa, Kpler, Precise Intelligence da kuma dandalin bibiyar jiragen ruwa. Rahoton ya bayyana cewa wata tanka ta ɗauki jirgin man fetur daga matatar Ɗangote ta fitar da shi zuwa gaɓar ruwan Togo.

Rahoton ya bayyana cewa CL Jane Austen ya ɗauki ganga fiye da 300,000 daga Ɗangote kuma ya yi tafiya zuwa yammacin Afirka. Idan za a iya tunawa, a watan da ya gabata, shugaban hukumar man fetur ta Ghana, Mustapha Abdul-Hamid, ya bayyana cewa Ghana na duba yiwuwar sayen mai daga matatar Ɗangote domin rage yawan kuɗin da ake kashewa wajen shigo da mai daga Turai wanda ya kai kimanin dala miliyan 400 a kowane wata.

A cewar shugaban NPA na Ghana wanda ya yi magana a taron OTL Africa Downstream Oil Conference a Legas, sayen mai daga Nijeriya zai rage farashin sauran kaya da ayyuka saboda cire kuɗin jigilar kaya. Ya ce, “Idan matatar ta kai ƙarfin tace ganga 650,000 a kowace rana, ba Nijeriya kaɗai za ta iya amfani da wannan adadi ba. Don haka, zai fi sauƙi mu dinga shigo da mai daga Nijeriya maimakon daga Turai, kuma hakan zai rage farashin mai a ƙasar.”

Haka zalika, jaridar The Punch ta ruwaito makonni biyu da suka gabata cewa matatar na shirin fara fitar da man fetur zuwa ƙasashen Afrika ta Kudu, Angola da Namibia. An kuma bayyana cewa sauran ƙasashen Afrika huɗu, Jamhuriyar Nijar, Chadi, Burkina Faso da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun fara tattaunawa da matatar kan yiwuwar samun man fetur daga Ɗangote.

A cewar wata majiya mai tushe, ta tabbatar da cewa matakin tattaunawa ya yi nisa tsakanin matatar mai ta Ɗangote da ƙasashen Ghana, Angola, Namibia, da Afrika ta Kudu, yayin da aka fara tattaunawar farko da Nijar, Chadi, Burkina Faso da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Majiyar ta ƙara da cewa, “Zan tabbatar muku cewa tattaunawa ta yi nisa sosai da Ghana, Angola, Namibia da Afrika ta Kudu, yayin da ake fara shirin tattaunawa da sauran ƙasashen huɗu.”

Rahoton ya kuma bayyana cewa, yanzu jirgin man fetur yana a yankin Lome kusa da Togo, wurin da aka saba yin musayar mai tsakanin jiragen ruwa. Kodayake wannan fitar da mai daga Ɗangote kaɗan ce idan aka kwatanta da kasuwar man fetur ta duniya, amma yana nuna shirin matatar wajen fitar da man fetur mai yawa zuwa ƙasashen da ke wajen Nijeriya, abin da zai iya kawo canji a kasuwar yankin.

By ukarofi