
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Talata ne wata ɗaukar bidiyo ta nuna yadda wasu sojojin Nijeriya waɗanda acikin su har da Manjo-Janar suka riƙa lakaɗawa wani magidanci da matarsa duka a yankin Gwarimpa dake birnin tarayya Abuja.
Lamarin ya auku ne a lokacin da ma’auratan masu suna Mista Vershima Mker da Misis Lami Jennifer Iorvihi ke cikin motarsu.
An gano cewa an casa mijin ne sakamakon kere motar sojojin da abin hawan na su ya yi a lokacin da su ke tuƙi.
A lokacin da su ke bada ba’asi game da batun, ma’auratan sun ce wani mai suna Janar G.S. Muhammad da Koporal A. Abubakar sun sanya musu hankwaf tare da jefa su cikin wata mota, inda daga nan suka garzaya da su ofishin ƴan sanda dake Gwarimpa.
Sannan ana zargin cewa Janar ɗin ya umarci ƴan sandan su tsare su har sai ya bada umarnin sake su.
Haka nan lamarin ya yi kama da irin yadda ya faru a watan Yuli inda aka ga wani jami’in soja na dukan wani ɗan ƙasa a bainar jama’a saboda sanya kayan sojoji.
Saidai, wannan ɗabi’a ta jami’an ta haifar da cecekuce acikin al’umma da sanya alamar tambaya game da tsare gaskiya da adalci da kuma girmama ƴan ƙasa acikin sojojin Nijeriya.
Baya ga haka ne ma’auratan suka shigar da ƙara kotu inda suka nemi a kori babban sojan tare da neman a biya su tarar Naira miliyan 150 kan zargin aibanta doka da wulaƙanta su da aka yi.
