Gwamnatin Katsina za ta tallafa wa manoman rani a jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban hukumar kula da noman rani ta jiha, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir ya ce gwamnatin Dikko Raɗɗa ta sha alwashin tallafawa manoman rani domin samar da abinci a faɗin jihar.

Abdulkadir Andaje ya faɗi haka ne a yayin da ya ke gudanar da taron masu ruwa da tsaki a fanin noman rani,yace taron zai taimaka wajen samun adadin masu noman rani a jihar.

“Hukumar ta shirya wannan taro domin ta sami cikakken adadin masu noman rani a jihar “Abdulkarim Nasir ya ce .

Hakan zai ba gwamnatin jihar damar tattara bayanan manoman rani da zai bada dama a taimaka masu da kayan noma, shugaban ya faɗa.

Abdulkarim Nasir ya
bayyana cewa tuni aka horar da manoman rani da zasu gudanar da aikin, ya kuma yayi jawabi mai tsawo akan ƙoƙarin gwamnan jihar wajen tallafawa manoman jihar kan abinda ya haɗa da samar da takin zamani mai rahusa da injinan ban ruwa da kuma maganin feshi.

Ya kuma nuna godiyar shi ga gwamna malam Dikko Raɗɗa bisa goyan baya da haɗin kai da ya ke bai wa hukumar don tabbatar da samun nasararta.

By ukarofi