ICPC za ta fara bin diddigin kwangilolin ayyukan mazaɓu a jihohi 21

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar ICPC ta fara bibiya ta bakwai kan aiyukan mazaɓu inda ta ke bibiyar aiyuka sama da 1,500 da aka ƙiyasta sun kai kimanin ₦610 biliyan. Kakakin ICPC, Demola Bakare, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Abuja.

A cewar Bakare, wannan shiri na bibiya wani tsari ne da hukumar ta ICPC ta ƙaddamar tun a shekarar 2019. An mayar da hankali kan yadda ake amfani da kuɗaɗen da aka ware wa ɓangarori masu muhimmanci kamar ilimi, lafiya, noma, albarkatun ruwa, wutar lantarki da sauransu.

Shirin bibiya zai shafi hukumomin gwamnati, ciki har da hukumomin tallafi irinsu hukumar raya yankin Arewa maso Gabas (NEDC) da hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC). Wannan tsari yana da nufin inganta bin ƙa’ida wajen aiwatar da aiyukan gwamnati, ƙara samun daraja daga kudin da aka kashe tare da tabbatar da bin ƙa’idodin da aka tsara a cikin takardun kwangila.

Sanarwar ta bayyana cewa, bibiya na bakwai zai shafi hukumomi irinsu hukumar ,NEDC, NDDC, NALDA, UBEC, REA, NPHCDA da TETFUND

Shirin bibiya na bakwai, wanda ya ƙunshi aiyuka 1,500 da darajarsu ta kai ₦610 biliyan, ya fara ne a ranar 18 ga watan Nuwamba a Abuja da wasu jihohi 21 da ke cikin yankunan ƙasar guda shida. Jihohin da za a gudanar da shirin a cikinsu sun haɗa da Kwara, Neja, Kogi, Kebbi, Kano, Kaduna, Jigawa, Bauchi, Gombe, Borno, Legas, Ondo, Osun, Oyo, Akwa Ibom, Ribas, Kuros Riba, Delta, Imo, Abia da Enugu da kuma babban birnin tarayya Abuja.

By ukarofi