
Daga BELLO A. BABAJI
Wani rahoton ofishin kula da kuɗaɗe na ƙasa ya bankaɗo wata zaftara da aka yi wa asusun kuɗin Ma’aikatar Ayyuka ɓangaren gine-gine ba bisa ƙai’da ba da ta kai kimanin Naira biliyan 4.6.
An gano hakan ne acikin rahoton shekara-shekara da ofishin Audita Janar na Ƙasa ya saba fitarwa, waɗanda daga ayyukan shekarun 2020 da 2021 ne aka same su tare da giɓi mai faɗi a lokacin Minister Babatunde Fashola.
Takardar ta zayyano bayanai da dama da aciki akwai batun biyan wasu kuɗaɗe ba tare da cike wasu ƙa’idodi ba, da ɓatar kuɗaɗen da suka haura kasafi da kuɗaɗen da suka haura waɗanda aka tabbatar da ware su da kuma bada wasu ƙwangiloli ba tare a bin ƙa’idodi ba.
Rahoton Auditan ya kuma bayyana hakan a matsayin sakaci daga ɓangaren gudanarwa na Ma’aikatar tare da gargaɗin akwai yiwuwar a iya rasa su baki ɗaya.
Duk da aika takardun tuhuma game da lamarin, Ma’aikatar ba ta bada ba’asi ba game yadda hakan ya kasance ba.
Haka kuma, Auditan ya bada shawarar cewa lallai ne babban sakataren ya tabbatar da halin da kuɗaɗen ke ciki tare da mayar da su asusun ƙasa.
Ya ƙara da cewa rashin bai wa asusun ma’aikata kulawar da ta dace wanda shi ke haifar da samuwar irin hakan, saɓa wa doka ne da kuma cin mutuncin aiki ga waɗanda aka ɗora wa alhakin hakan.
