
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar masu gidajen yaɗa labarai ta ƙasa (BON) ta ce ba ta amince da cin mutunci da wulaƙanta harkar jarida ko ƴan jarida da gwamnati ko jami’anta ke yi ba.
Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da ƙungiyar manema labarai ta Arewa ta rubuta wani saƙo ga hukumomi game da maka Shua’ibu Mungadi da Tijjani Ramalan da wasu gidajen jaridu a kotu da ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya yi kan zargin ɓata suna da yaɗa bayanai masu tunzurawa.
BON ta ce za ta haɗe kai da sauran ƙungiyoyin al’umma don kare mutuncin ƴan jarida da ba su damar cigaba da ayyukansu yadda ya kamata.
Ƙungiyar ta yi ikirarin zama jagaba wajen tabbatar da kare haƙƙin ƴan jaridan daga jami’an gwamnati a idon al’umma.
Tuni dai ƙungiyar ta ce ta sanar da mambobinta a ƙungiyoyi da gidajen jaridu.
