“Ina rubutu ne don samun natsuwa a zuciyata”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Ga duk waɗanda suka karanta littattafan Hausa a wajejen farkon shekarun 2000 zuwa 2010 ba za su kasa karanta littattafan Hafsat C. Sodangi ba, wata marubuciya daga garin Jos. Hajiya Hafsat Sodangi ta yi fice wajen rubuta ƙirƙirarrun labarai da suka shafi zamantakewar ma’aurata, soyayya da kishi a tsakanin mata. Tana daga cikin marubutan da suka ci gajiyar rubutu a shekarun baya, kuma a yanzu ma da galibin marubuta suka koma rubutu ta onlayin, littattafanta suna cigaba da samun karɓuwa. Kawo yanzu marubuciyar ta rubuta littattafai aƙalla 31, kuma har yanzu tana cigaba da fitar da sabbin labarai. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba AbubakarYakubu, ta shaida masa yadda aka yi ta fara rubutu domin furzar da abin da ke ƙunshe a ranta, daga bisani kuma Allah Ya sa wa abin albarka har ya zama sanadin ɗaukakarta.
MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki.
SODANGI: Sunana Hajiya Hafsat Chindo Sodangi, ina auren Alhaji Yunusa Abdullahi, da ke zaune a Unguwar Sarkin Mangu kusa da makarantar School for Higher Islamic Studies a garin Jos. Ina da yara huɗu, mata biyu maza biyu. Ni marubuciyar littattafan Hausa ce, kuma ‘yar kasuwa. Na fara fitar da littattafaina a shekarar 2002, da littafin ‘Uwar Miji’.
Ki ba mu tarihin rayuwarki.
Da farko dai an haife ni ne a shekarar 1970, shekaru 54 kenan, a wata rugar Fulani da ke ƙauyen da ake kira Kuru, a yankin ƙaramar Hukumar Barikin Ladi da ke Jihar Filato, a wancan lokacin. Amma a yanzu ƙauyen ya koma ƙarƙashin ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu. Mahaifina bafulatani ne mai kiwon shanu, wanda yake tashi daga wannan wuri ya koma wancan. Amma daga bisani ya koma cikin Jos, inda ya zauna wuri ɗaya domin kula da iyalinsa, da kuma sanya su a makaranta don su samu ilimi mai inganci. Ta haka ni ma na samu dama na taɓa nawa karatun, kodayake ban yi nisa ba aka yi min aure. Allah cikin ikonsa wannan karatu da na yi shi ne ya zame min tsani wajen cigaba da karatuna na addini a School for Higher Islamic Studies, da kuma rubuce-rubuce da na riƙa yi.
Wanne ƙalubale kika fuskanta da ya koya miki wani muhimmin darasi a rayuwarki?
Akwai ƙalubale masu yawa gaskiya, kuma dama ai ita rayuwa kullum cikin gwargwarmaya ake yin ta, daga wannan a koma wancan. Wasu ma na ganin ita ɗin tamkar wani littafi ne mai shafuka da yawa, kowanne shafin ka buɗe da abinda za ka karanta.
Wanne abu ne za ki iya cewa, ya taimaka wajen mayar da ke irin macen da yanzu kika zama?
Kakkyawar tarbiyyar da na samu daga wurin iyayena, uwa da uba, (Ubangiji Allah Ya gafarta musu). A dalilin kulawarsu da halayensu na ƙwarai ne ya sa na zama duk wani abu da na zama a rayuwata.
Mene ne ya ja hankalinki kan rubutun adabi?
To, da yake na fara rubutu ne tun da ƙuruciya sosai, zan iya cewa a lokacin kamar ina rage wa zuciyata wani nauyi ne. Idan aka yi min wani abu da ya dameni a raina ba na iya faɗa wa kowa, saboda a wancan lokacin ni ba mai son yawan magana ba ce. Sai abu ya yi ta kai kawo a raina yana damuna, amma a hankali na gane idan ina rubuta abin da ke zuciyata a takarda ina samun sauƙin matsalar. Da haka ne rubutu ya zama ɗabi’ata, tun ina yi ina ƙonawa don kar a gani, har ya zama ina ajiyewa, don in an gani an karanta ana yabawa. Ganin an fara kwaɗaitar da ni kan in shiga rubuta labarai, sai na fara samun ƙwarin gwiwa har na cigaba da rubutu. Tun daga wancan lokacin har kawo yanzu dai muna bugawa, kuma Alhamdulillahi.
Kawo yanzu kin rubuta littattafai guda nawa? Kawo sunayensu da bitar wasu daga ciki.
Na rubuta littattafai sun kai 31. Daga ciki akwai, ‘Wata Fuskar’, ‘Duk ɗaya’, ‘Uwar Miji’, ‘Mai ɗaki’, ‘In Kunne Ya Ji’, ‘Wayyo Duniya’, ‘Abu Naka’, ‘Wace Ce Ni?’ ‘Yi Wa Wani’, ‘Tabbataccen Al’amari’,
‘Garin Banza’, ‘Halin Rayuwa’, ‘Mijin Tace’, da kuma ‘Kyautatawa’.
Sauran sun haɗa da, ‘Daga ƙin Gaskiya’, ‘Da Kamar Wuya’, ‘Gani Gareka’, Biyan Buƙatar Rai, ‘Nufin Allah’, ‘Kifi Na Ganinka’, ‘Shamaki’, ‘Mai Uwa’, ‘Na Ga Ta Kaina’, ‘Rabon Kwaɗo’, ‘Cikar Alƙawari’, ‘Bugun Zuciyarmu ɗaya’, da kuma, ‘Me Za Mu Ce Da Maza?’
Wanne littafin ne ya fara ɗaga sunanki a tsakanin marubuta?
Littafina na biyu wanda ya fita a ƙarshen 2003 mai suna ‘Naga Ta Kaina’ shi ne ya ƙara fitar da sunana har jama’a da dama suka sanni.
Yaya alaƙarki da masu karatun littattafanki, ta yaya kike mu’amala da su?
Alhamdulillahi, muna da kakkyawar alaƙa da mu’amala ta mutunta juna, da girmamawa, ƙauna da kuma zumunci mai ƙarfi. Muna yawan gaisawa ta waya, wani lokaci kuma har gida suna kawo min ziyara.
Wanne abin farinciki ko akasin haka ne ya taɓa faruwa da ke ta sanadiyyar rubutu wanda ba za ki manta da su ba?
Gaskiya abin farincikin ma shi ya fi yawa, na samu alheri sosai ta dalilin rubutu, har ba zai yiwu in tsaya ina bayani ba. Babba daga ciki dai da ya fi kowanne muhinmanci a wurina shi ne saduwa da jama’a. Kullum ina faɗa cewa mafi girman abin da na samu a rubutu shi ne arziƙin jama’a, don mutum rahama ne. Kuma Alhamdulillahi na samu, an godewa ubangiji.
Game da akasin haka kuwa, zan iya cewa akwai wani abu da ya taɓa faruwa da ni wanda ba zan manta da shi ba, duk da shima an yi sa’a ba wani abu mai tsanani ba ne ya faru. Akwai lokacin da na rubuta littafin ‘Mijin Tace’, wasu suka zo har gida suna ƙorafin wai na yi amfani da sunan mahaifinsu da gidansu da unguwarsu, da abubuwan da suka faru, saboda kwatancen da na yin komai ya zo ɗaya da rayuwar gidansu. To, amma ni na san ba labarinsu na ɗauka ba, ƙirƙira ta ce kawai, arashi ne kawai aka samu. Kuma Alhamdulillahi, bayan na yi musu bayani a nutse, sun fahimci ba da gangan na yi ba. Don haka gaskiya zan iya cewa ban fuskanci wani abu mara daɗi ba kan harkar rubutu in ba wannan ba. Alhamdulillahi.
Ta yaya ki ke samun jigon da ki ke rubutu a kai?
To, kamar yadda na faɗa a farko lokacin da nake bayani kan yadda na fara rubuta littafi, inda na ce ina rubutu ne domin fitar da abubuwan da ke raina, don samun natsuwa a zuciyata. Wannan ɗabi’ar ce ta koya min rubutu kan abinda na gani da idona ko na ji da kunnena. Bisa wannan dalili ne littattafaina na farko suka zama yawancin su labarin da ya faru ne. Misali kamar littafin ‘Naga Ta Kaina,’ da ‘Auren Dole,’ wanda labari ne da ya faru da gaske, inda wata yarinya ta ƙi bin umurnin ubanta har ta ƙona kanta da wuta, aka yi jinyar ta har ta warke. Sai aka ce ta kawo wanda take so ɗin, shi kuma da ya zo ya ce tafi ƙarfin shi don shi umurnin ubansa yake bi. Wannan dalilin ne ya yi sanadin barin yarinyar nan daga gida saboda baƙinciki. Shi ne ni kuma na juya abin da ya faru zuwa labari, don ya koya wa yara darasi. A cikin littafin mun ga yadda aka yi wani auren dole wanda miji ba ya so ita ma matar ba ta so, amma da suka yi biyayya sai suka ci nasara.
Shi ma littafin ‘Wayyo Duniya’, mutuwa na gani, wacce ta tarwatsa gida, sakamakon rashin tsayayye wanda zai tsawatar a cikin iyali. Haka kuma shi ma littafin, ‘Abu Naka’, auren zumunci aka yi aka kuma ɓata akan hakan, sai na kawo misali na zumuncin gaskiya shi ne wanda mutun ba ya komawa ya goyi bayan nashi, da dai wasu da dama.
Amma wannan ba yana nufin ban yi wasu ƙirƙirarrun labarai ba ne, a’a, na yi su da yawa, irin su ‘A Yi Dai Mu Gani’, ‘Mata Masu Duniya’, ‘Shamaki’, ‘Duk ɗaya’, ‘Wata Fuskar’, da wasu ma da yawa.
Wanne salon rubutu ne ya fi baki sha’awa, almara, yaƙe-yaƙe, sarauta, ko soyayya?
To, ai ni zan iya cewa akasarin rubutuna yana kan layin soyayya ne, don haka shi ya fi bani sha’awar rubutawa. Kodayake, babu ta inda ba na juya alƙalamina don ya isar da saƙon da nake son isarwa ga masu karatu. Ko a yanzu haka na kammala rubuta sabon littafin da na yi, wanda ban riga na sake shi ba, wanda na rubuta da salo na daban, da ba shi aka saba gani daga wajena ba. Amma in sha Allahu idan ya fito za a gani.
Mene ne sirrin da ki ka riƙe wanda ya sa tsawon lokaci har yanzu tauraruwar ki tana haskawa a tsakanin marubuta?
To, ni ba zan ce ga wani sirri da na riƙe ba, illa iyaka nasan duk wani al’amari daga Allah yake. Muhimmin abu dai shi ne gyara aikin ka, kuma ka yi rubutu mai inganci. In za ka yi rubutu ka tabbatar labarin da za ka bayar mai ma’ana ne, kuma ya zamana akwai wani darasi da yake bayarwa ba nishaɗi kawai ba.
Bayan jinkiri na wani lokaci ba a ganin sabbin littattafanki, me ya ja hankalinki ki ka sake dawowa fagen rubutu?
Nacin mutane. Masoya da masu bibiyar littattafaina kusan kullum sai sun kira ni, adadin da ba zan iya faɗa ba. Suna yawan kirana su ce mini “Auntie Hafsat, ki dawo, ki dawo.” Kusan kowanne lokaci aikin kenan, har kuma dai na dawo din, da yake ubangiji ya ƙaddara za a yi hakan. Alhamdulillahi.
Idan za ki auna da cigaban da kike samu a baya lokacin da kike buga littattafanki da kanki, da yanzu kuma da kasuwar ta koma manhajojin sayar da littattafai, wanne ya fi kawo miki cigaba?
Shi ɗan’adam kowa yana da zamaninsa. Ni marubuciya ce da zan ce Alhamdulillahi, kowa yasan littattafaina suna cikin littattafan da suka yi kasuwa, kuma suka samu karɓuwa a wajen masu karatu. Don haka duk da rashin tsarin tafiyar da al’amuran kasuwancin littattafai a yanzu, ni tawa kasuwar ta yi kyau sosai, don haka ba zan yi ƙorafi ba. Matsalar da na yi ta fuskanta a baya bata hana nasara ta ba. Yanzu muhimmin abu a wurina shi ne an yi wancan zamanin tare da ni, yanzu ma kuma ana yi da ni sosai, don ina cikin tsarin rubutun onlayin tsudum. Don haka zan iya cewa, kamar na ci jiya ne kuma ga shi ana cin yau tare da ni. A wajena duk wani cigaba cigaba ne.
Shin kina ganin har yanzu akwai damar sake dawo da wallafar littattafai?
Zan iya cewa, E, abu ne mai yiwuwa. Kodayake akwai buƙatar samar da gyare-gyare masu yawa.
Shin a yaranki akwai wanda ke da sha’awar rubuce-rubuce irin naki? Kuma za ki so wani ya gaje ki a cikinsu?
To, da yake yanzu dukka yaran sun girma, wasu sun zama ma’aikata wasu sun yi aure suna kuma da iyalai a gidajen aurensu. Babu wanda ya nuna yana da ra’ayin hakan, wataƙila saboda hidimomin karatu da rayuwa, hankalinsu bai kai can ba.
Yanzu sai dai ko a yi tunanin samu a cikin jikoki, domin shi rubutu wani abu ne da ba kowa ke yi ba. Idan wata a cikinsu ta nuna tana sha’awar yin rubutu, zan yi farinciki sosai!
Mece ce shawararki ga matasan marubuta na wannan lokaci?
To, shawarata garesu shi ne su yi rubutu mai ma’ana, su kaucewa rubutun batsa, domin shi wannan rubutu da muke yi watarana za a karanta shi ko bama nan, don haka mu yi ƙoƙarin bar wa ‘yan baya abin koyi mai kyau.
Yaya harkar rubutun adabi take a garin Jos, wanne cigaba ake samu?
Alhamdulillahi, zan iya cewa an samu cigaba mai yawa, domin a wancan lokacin namu babu marubutan sosai, yanzu kuwa akwai su da yawa, har ma suna kafa ƙungiyoyi, don taimakon kansu da kansu. Ka ga kenan ana samun cigaba sosai.
Yaya kike ganin za a inganta zumunci a tsakanin marubuta?
Ta hanyar inganta mu’amala da juna. Domin babu wani zumunci da za a iya sadar da shi matuƙar babu mu’amala mai kyau a tsakani.
Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?
Abinda ka shuka, shi kake girba!

