An zargi wasu ‘yan Boko Haram da kai wa tawagar jami’an hukumar tsaro ta NSCDC hari a yankin Farin Ƙasa na ƙaramar hukumar Chukun, Jihar Kaduna. Lamarin ya faru ne ranar Litinin yayin da jami’an ke duba layukan wutar lantarki na Ƙasa a Shiroro, Jihar Neja, sakamakon hare-haren da suka haddasa yankewar wuta a yankin Arewacin Nijeriya.
Mai magana da yawun NSCDC, DCC Afolabi Babawale, ya bayyana cewa tawagar ta ƙunshi jami’ai tara da wasu ma’aikata 71 da aka tura domin kare muhimman kayayyakin gwamnati. Yayin da suke sintiri a wuraren da ake ganin suna da rauni, sun yi arangama da wasu baƙin haure a kusa da ƙauyen Dagwachi kuma suka ba su tsaro tare da tawagar. Ba tare da sun sani ba, fiye da mayaƙan Boko Haram 200 sun musu kwantan ɓauna saman tsauni inda suka kai musu harin.
Duk da yawan mayaƙan, jami’an NSCDC sun nuna jarumta wajen mayar da martani, inda suka kashe fiye da ‘yan ta’adda 50 a musayar wuta. Sai dai harin ya yi sanadiyyar ɓacewar jami’ai bakwai, wanda hakan ya sa aka fara gaggawar neman su a cikin daji. Wasu da suka ji rauni suna karɓar magani a asibiti.
A nasa ɓangaren, Shugaban NSCDC, Ahmed Audi, ya yi Allah-wadai da harin, yana mai kira da cewa hakan ba komai ba ne face mugun nufi ga jami’ai masu sadaukarwa da kare al’ummar Ƙasa. Ya yaba da jarumtar jami’an tare da tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da tsare muhimman kayayyakin Ƙasa a duk inda suka samu barazana.
