A ranar Laraba, Majalisar Dattawa ta tsige Shugaban Kotun ɗa’ar ma’aikata (CCT), Ɗanladi Umar, daga muƙamin sa. An tsige shi ne ta hanyar amfani da sashe na 157(1) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999.
Wannan sashe ya tanadi cewa kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisar dattawa na iya tsige shugaban kowanne hukuma mai zaman kanta da ake zargi da aikata laifukan da suka saɓawa doka da kuma rashin ɗa’a a lokacin aikinsu.
Aƙalla Sanatoci 84 daga cikin 107 da ke aiki a yanzu sun sanya hannu don tsige Ɗanladi Umar, wanda ke fuskantar tuhume-tuhume da dama.
Ƙarin bayani na nan tafe…
