Rundunar Sojojin Nijeriya ta fara bincike kan wani bidiyo da ya bayyana a kafafen sada zumunta, wanda ke nuna wani Babban Janar da wasu sojoji suna ci zarafin wasu ma’aurata a birnin tarayya, Abuja. An ce lamarin ya faru ne bayan da sojojin suka tsayar da ma’auratan saboda sun yi ƙetare da ba bisa ƙa’ida ba a gaban tawagar motocinsu.
A bidiyon, an ga sojojin suna cin zarafin ma’auratan, kafin daga bisani suka ɗaure su da ankwa sannan suka kai su ofishin ‘yan sanda da ke Gwarimpa. Rahotanni sun ce sojojin sun umurci ‘yan sandan da su tsare ma’auratan ba tare da lokaci ba. Wannan ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta kan yadda lamarin ya wakana.
Mai magana da yawun Rundunar Sojojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa Babban Hafsan Sojojin Ƙasa mai rikon kwarya, Olufemi Oluyede, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan wannan lamarin. Ya ce, An samu rahoton wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ke nuna wani babban jami’in soja da wasu sojoji biyu suna taƙaddama da wani namiji da mace a cikin birnin Abuja.
Sanarwar ta ƙara da cewa har yanzu ba a tantance dalilan da suka kai ga aukuwar wannan lamari ba. Rundunar ta yi alƙawarin gano gaskiyar al’amarin tare da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da adalci.
