
Daga BELLO A. BABAJI
Ana tsammanin ƴan Nijeriya dake zaune a wasu ƙasashen waje su samu damar kaɗa ƙuri’a yayin zaɓe bayan da ƙudirin kwaskwarima ga dokar ƙasa da za ta bada damar hakan ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilai, a ranar Laraba.
Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas ya ɗauki nauyin ƙudirin wanda ke neman a yi gyare-gyare ga dokar zaɓe ta 2022 da zai sa mazaunan waje su samu damar yin zaɓe.
A watan Yuli ne aka miƙa ƙudirin don yi masa karatu na biyu ga kwamitin da ke kula da lamuran da suka shafi zaɓe na majalisar don tantancewa.
Bayan tsallake karatu na biyun ne ake sa ran hukuncin kwamitin ya bai wa ƴan wajen damar yin zaɓe.
