Gwamna Lawal ya ba da tabbacin goyon baya ga shugabannin Jami’ar Tarayya ta Gusau

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ba da cikakken goyon baya ga Jami’ar Tarayya ta Gusau (FUGUS). Ya bayyana haka ne yayin karɓar tawagar kwamitin gudanarwar jami’ar ƙarƙashin jagorancin shugaban kwamitin, Rt. Hon. Injiniya Aminu Sani Isah, wanda suka kai masa ziyara a gidan gwamnati ranar Talata.

A cewar mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, kwamitin gudanarwar jami’ar ya yaba wa gwamnan bisa irin goyon bayan da yake bayarwa ga jami’ar. Gwamna Lawal ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa jami’ar saboda rawar da take takawa wajen bunƙasa cigaban al’umma.

Yayin jawabinsa, Gwamna Lawal ya bayyana farin cikinsa kan shirin jami’ar na fara karatun likitanci (MBBS). Ya ce, “Mun yi aiki tuƙuru wajen ɗaukaka asibitin mu na musamman zuwa asibitin koyarwa don tabbatar da cewa suna da kayan aiki na zamani da za su dace da buƙatun karatun ku.” Ya ƙara da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin samar da filin gine-gine don ɗalibai da kuma warware batutuwan diyya na filaye tare da jami’ar.

Tun da farko, Shugaban kwamitin gudanarwar jami’ar, Rt. Hon. Aminu Sani Isah, ya yaba wa Gwamna Lawal bisa irin ayyukan alheri da ya yi wa jami’ar, tun ma kafin ya zama gwamnan Zamfara. Ya bayyana cewa wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen bunƙasa harkar ilimi da cigaban al’ummar jihar.

By ukarofi