Majalisar Wakilai ta watsar da ƙudirin wa’adin shekara shida ga Shugaban ƙasa da gwamnoni

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Wakilai ta ƙasa ta ƙi amincewa da karatu na biyu na ƙudirin da ke neman samar da wa’adin shugabancin shekaru shida kacal ga Shugaban ƙasa da gwamnoni.

Majalisar ta yi watsi da ƙudirin ne yayin zamanta na ranar Alhamis.

ƙudirin dai an gabatar da shi ne ƙarƙashin jagorancin ɗan majalisa Ikenga Imo Ugochinyere tare da sauran mambobi 33.

An gabatar da ƙudirin domin karatu na biyu ne daga babbar mai ɗaukar nauyinsa, Ugochinyere, sannan aka goyi bayan hakan.

Sai dai, yayin da Kakakin Majalisar, Abbas Tajuddeen, ya miƙa ƙudirin don kaɗa ƙuri’a ta baki, muryoyi masu cewa “A’a” sun fi yawa daga mambobin majalisar.

A ƙarshe, Kakakin ya sanar da cewa waɗanda suka ce “A’a” sun yi rinjaye, wanda hakan ya nuna cewa ƙudirin bai samu amincewa ba kuma ya faɗi a karatu na biyu.

By ukarofi