Tinubu na shirin naɗa sabbin jakadun Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta fara shirin tura jami’an ofishin jakadanci zuwa ofisoshin diflomasiyya a duniya kafin a naɗa sabbin jakadu.

Shekara guda da wata ɗaya kenan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo da jakadun Nijeriya gida. Tun bayan dawo da su ranar 2 ga Satumba, 2023, ofisoshin jakadancin Nijeriya 109 a ƙasashen waje sun kasance babu cikakken wakilci na jakadanci. 

Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce jakadun sun yi aiki ne bisa umarnin shugaban ƙasa a cikin ƙasashen da suka karɓi baƙuncinsu kuma “ikon shugaban ƙasa ne ya aika ko kiran su daga kowace ƙasa.”

Tuggar ya ƙara da cewa, yana daga cikin dabarun da ake bi na daidaita al’amuran Nijeriya a ƙasashen waje.

An yi wannan kiran ne amma ya bar baya da ƙura a diflomasiyya saboda ba a sanar da waɗanda za su maye gurbinsa ba tun daga lokacin.

Sai dai jinkirin da aka samu wajen naɗa waɗanda za su gaje su ya haifar da damuwa.

A watan Afrilun 2024, gwamnati ta naɗa manyan jami’ai 12 da kuma manyan muƙamai biyar don wakiltar Nijeriya a ƙasashe 14, amma waɗannan matakan wucin gadi sun gaza cike giɓin shugabanci a muhimman ayyuka.

A ranar 28 ga watan Mayu, ministan harkokin wajen ƙasar ya amince da lamarin, inda ya bayyana rashin kuɗi a matsayin dalilin da ya sa aka jinkirta naɗa sabbin jakadu.

By ukarofi