Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Matatar man Ɗangote ta ɗora daga inda ta tsaya wajen sayen ɗanyen mai daga ƙasar Amurka a ci gaba da ƙoƙarin da ta ke yi na samar da wadataccen mai da kuma inganta aikin tace manta.
Lamarin ya zo ne bayan dakatar da sayen ɗanyen mai daga ƙasashen ƙetare na tsawon watanni uku, inda aka mayar da hankali wajen sayen na cikin gida Nijeriya.
Wani rahoto da Bloomberg ta fitar a ranar Larabar da ta gabata ya ce, za a kai gangar ɗanyen mai ta WTI Midland miliyan biyu daga Cheɓron Corp zuwa matatar Dangote a wata mai zuwa.
Wannan sabon lamari na iya zama manuniyar cewa, shirin nan na ‘sayen ɗanyen mai da Naira’, wanda Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta gabatar ya samu tsaiko ko kuma matatar man ba ta samun isasshen ɗanyen man fetur daga Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC).
“Matatar Dangote ta sayi man fetur na farko a Amurka bayan shafe watanni uku ana ci gaba da haƙowa. Kamfanin ya sayi kusan ganga miliyan biyu na WTI Midland na ɗanyen mai daga Cheɓron Corp,” inji rahoton.
Chevron ya ba da babban jirgin ruwa Azure Noɓa don yin lodin ɗanyen mai daga Tekun Fasha na Amurka a ranar 5 ga Disamba zuwa Dangote, kamar yadda na’urorin da Bloomberg suka gani.
