An kama ɗan ƙasar Aljeriya bisa zargin safarar makamai ga ‘yan bindiga a Zamfara 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

‘Yan sanda a Zamfara sun kama wani ɗan ƙasar Aljeriya mai shekaru 58 da ake zargi da safarar makamai ta kan iyaka.

Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa ya rawaito cewa Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mohammed Dalijan, ne ya bayyana hakan a Gusau ranar Talata.

Ya ce ‘yan sanda sun ƙwato bindigogi AK47 guda 16 yayin wasu samame daban-daban da suka gudanar cikin makonni uku da suka gabata.

Har ila yau, ya bayyana cewa rundunar ta ƙwato bindiga mai bututu biyu da wata bindiga da aka ƙera a gida daga wani da ake zargi da ƙera makamai a Jos, Jihar Filato.

”Rundunar, bisa samun bayanan sirri, ta bi sawun wani mai ƙera makamai a Jos kuma ta kama wani ɗan safarar makamai daga Aljeriya a iyakar Illela.

”Wanda ake zargi ɗan Aljeriya ya shaida wa ‘yan sanda cewa yana aikata wannan laifi tsawon shekaru takwas.

”Wanda ake zargin yana ba da makamai da alburusai ga ‘ya bindiga a dukkan jihohin yankin arewa maso yamma.

”Lokacin da aka kama shi, an ƙwato bindigogi AK47 guda huɗu daga gare shi,” in ji shi.

Dalijan ya ce ‘yan sanda sun kuma kama wasu mutane da ake zargi, ciki har da masu safarar babura ga ‘yan bindiga.

”‘Yan sanda sun ƙwato alburusai da ke da rai da kuɗi Naira miliyan 2.5 daga hannun waɗanda ake zargi, da sauran kayayyaki,” in ji shi.

Haka nan, kwamishinan ya ce sun kama wasu masu haƙar zinariya ba bisa ƙa’ida ba tare da ƙwato wasu injinan tono kasa masu yawa.

Kwamishinan ya gargaɗi jama’a cewa haramcin da Gwamnatin Tarayya da ta jiha suka sanya kan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba har yanzu yana nan daram.

By ukarofi