
Daga BELLO A. BABAJI
A sati mai zuwa ne Gwamnatin Tarayya da gwamnoni za su yi hukunci game da samar da ƴan sandan jihohi.
Gwamnan Jihar Bayelsa, Duoye Diri ya bayyana hakan wa manema labarai a Fadar shugaban ƙasa dake Abuja, bayan kammala taron Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa (NEC).
Ya ce, Majalisar ta bai wa jihohin Adamawa da Kebbi da Kwara da kuma Abuja mako guda (28 ga watan Nuwamba) su gabatar da matsayarsu game da lamarin.
Diri ya ce a yayin zaman majalisar na mako mai zuwa ne, za a cimma matsaya.
A ranar 15 ga watan Fabrairun shekarar nan ne Gwamnatin Tarayya tare da jihohin ƙasar suka fara maganar samar da ƴan sandan jihohi yayin wani zama na gaggawa tsakanin Shugaba Tinubu da gwamnonin a Fadar shugaban ƙasa.
A nasa jawabin, Ministan Labarai da Wayar da kan Al’umma, Mohammed Idris ya ce ana cigaba da bin hanyoyin da suka dace tare da shigo da masu-ruwa-da-tsaki don tabbatar inganci game da batun wanda a yanzu haka ake jiran rahoton sauran jihohi huɗu don cimma matsaya.
