Me ke taɓa lafiya?

Spread the love

Tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

Akwai abubuwa da yawa da ke da tasiri ga lafiyar mutum, yau za mu kalli wasu daga cikinsu

Yawan shan fruits (kayan marmari) ya na daƙile cutuka da yawa, ciki har da wasu nau’o’in ciwo daji 

Hutawa na inganta lafiya.Gajiya kala kala ce, akwai ta jiki akwai ta tunani. Dukkansu su na rage ingantacciyar lafiya 

Kudi ya na da babban tasiri ga lafiya. Idan akwai, za a ci mai kyau asha mai kyau, a biya kudin kula da lafiya gwaggwaɓa domin samun waraka akan lokaci. 

Dabi’a na da tasiri ga lafiya, imma ɗabi’ar cima ko ta bacci ko ta tunani. Ma’ana Abin da kake ci, da yadda kake bacci da yadda kake tunani

Da zarar nauyin jikinka ya wuce gwargwadon tsawonka da kuma shekararka, to hakan zai jefa ka cikin haɗarin samun wasu cututtuka irin su hauhawar jini. 

A lokacin da nauyin jikinka ya ke ƙaruwa fiye da ƙa’ida, ƙarfin tunaninka da kaifin basirarka raguwa ya ke. Binciken masana ne ya tabbatar da hakan. Na gode

Naku; MIAbdullahi

[email protected]

By ukarofi