Yahya ya zama sabon Shugaban NUJ na Nijeriya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), Kwamred Alhassan Yahya, ya zama sabon shugaban ƙungiyar na ƙasa.

Kwamred Alhassan Yahya ya samu ƙuri’u 436, inda ya kayar da wasu ’yan takara biyu a taron wakilan ƙungiyar na takwas da aka yi tsakanin Laraba da Alhamis a Owerri.

Shugaban kwamitin zaɓen, Mista Mike Ikeogwu, ne ya sanar da cewa ya yi nasara a safiyar ranar Alhamis.

Sauran ’yan takarar kujerar shugaban na ƙasa, Bamidele Atunbi da Garba Mohammed, sun samu ƙuri’u 97 da ƙuri’u 39 da suka zo na biyu da na uku.

Da yake bayyana sakamakon, Ikeogwu ya ce, “a bisa ikon da aka ba ni a matsayina na shugaban kwamitin zaɓe, Ina bayyana cewa, Alhassan Yahya, bayan da ya samu ƙuri’u mafi yawa, ya lashe zaɓen a matsayin Shugaban NUJ na tsawon shekaru uku masu zuwa.”

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Kwamred Yahya, wanda ke aiki da Kamfanin Kafafen Yaɗa Labarai na Gombe, shi ne Shugaban NUJ na farko daga yankin Arewa maso Gabas.

A jawabin da ya yi na karɓar muƙamin, ya yi alƙawarin yin hidima “cikin tawali’u da tsoron Allah” tare da “bin tsarin mulkin NUJ da dukkan adalci, gaskiya da riƙon amana.”

Ya gaji Cif Chris Isuguzo daga Kudu maso Gabas, wanda ya yi wa’adi biyu na shekaru shida.

An dawo da sabon mataimakin shugaban na kasa, Abimbola Oyetunde, wanda shi ne babban manajan gidan rediyon Nijeriya Bronze FM, Edo, ba tare da hamayya ba a wajen taron.

A zaɓen ta, Oyetunde, tsohuwar mamba a kwamitin amintattu na ƙungiyar ta zama mataimakiyar shugaban ƙungiyar ta NUJ mace ta farko ta ƙasa.

Sauran jami’an na ƙasa da aka mayar da su ba tare da hamayya ba sun haɗa da Ma’ajin ƙasa, ɓictor Ndukwe (tsohon Shugaban Majalisar Abia), da Ronke Samo, Mataimakin Shugaban Shiyya ta B (Kudu maso Yamma).

Haka kuma an zaɓi Eze Adiukwu, Sakatariyar shiyyar (Kudu maso Gabas) na ƙungiyar ba tare da hamayya ba.

By ukarofi