Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta samarwa da ƙabilar Sayawa dake jihar buƙatar da ta yi katutu a zukatansu na tabbatar masu da masarautar gargajiya kafin saukarsa daga kujerar mulki, wacce za ta kai gaci a shekara ta 2027.
Sanata Bala Mohammed ya yi waɗannan jawabai ne a kwanakin baya yayin da yake karɓan rahoton kwamitin samar da madafa kan batun ƙirƙiro masarauta wa ƙabilar Sayawa, yana mai cewar, wajibi ayi dukkan abinda ya kamata na samar wa Sayawa Basarake mai laƙabin ‘Gumza’ kamar yadda al’adar gargajiyarsu ta zayyana.
“Wannan batu ne da ya zamo ala-ƙaƙai shekara da shekaru sakamakon rashin jituwa dake wanzuwa a tsakanin al’ummomi, wanda ya zamo wajibi a kawo ƙarshensa. Kuma idan ba zan yi amfani da ƙwarewa ta da matsayina na kawo ƙarshen wannan matsala, Ina shakkar babu wani mutum da zai samar da warakarta,” inji Gwamna.
Bala sai ya ce, “Ina matuƙar jinjinawa ƙabilar Sayawa sakamakon ɗimbin goyon baya da suke bani tun lokacin da likkafa ta, ta cira zuwa matsayin sanata, har ya zuwa wannan lokaci da nake kan kujerar Gwamna wa’adi na biyu, suna tare da ni a zukatunsu.”
Gwamna Bala ya bayyana cewar, yana daga cikin buƙatar, ba a kafa masarautar Sayawa da wata matsala ko nakasu ba, la’akari da wanzar da kyakkyawan tsari, mazauni da tafarkin gudanar wa mai ɗorewa, ya sa ake tafiyar da lamarin cikin lura na yaƙini.
Ya yi waiwaye da cewar, rikicin ƙabilancin addini da ya laƙume magabatan gwamnatocin jihar Bauchi, daya faro tun a shekara ta 1991, ya Kuma tamɓarar da kwamitocin bincike na Ambassda Dada Chinade, Mai Sharia Bala Umar, da sauran su, har-ma da kassara wata doka da Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi ta kafa, biyo bayan rashin amincewa na masu ruwa-da-tsaki.
“Ina da yaƙinin wannan tsari zai bai wa kowa, har da mai azaɓarɓanin yiwa kansa shugabancin sarauta, damar fitowa takarar zaɓe ko naɗi. Wannan sahihin tsari na gabatar da al’amura, ba haka kawai mutum ya naɗa kansa shugaba ba, wancan tsarin ai dace ba.”
Gwamna Bala ya kuma yabawa ‘yan kwamiti bisa jajircewar su na ziyartar makwabta jihohin Filato, Kaduna da Nasarawa a yayin gudanar da ayyukan su, domin gane wa kawunan su yadda al’ummun waɗancan jihohi suke yin naɗa-naɗen sarakunan su.
Gwamnan na Bauchi sai ya yabawa kwamitin bisa kuzarin ta na sauke nauyin da aka ɗora mata, yana mai cewar, “Zanyi nazarin rahoton wannan kwamiti da idon basira. Na kuma umarci sakataren gwamnatin jiha ya gabatar da mutane kimanin guda 100 daga sassa dabam-dabam na al’umma domin ayi zama dasu bisa nazarin rahoton”.
“Idan a wannan mahaɗa aka samu waraka, lamari yayi kyau. Idan kuma ta kama mu waiwaici dokar da Majalisar Dokoki ta jiha ta kafa, Majalisar tana zaune bata gushe ba, domin gusar da duk wani tuntuɓe dake bisa hanya. Wannan shine tsarin da muke yin da’awa dashi, Wanda zai kai mu gaci.
“Muna ta wasan ɓoye tsakanin mu da Wani mutum daya aiyana kan sa a matsayin Basarake ‘Gumza’ ba tare da amincewar gwamnatin jihar, ko bin ka’ida ta hannun hukumar kula da ƙananan hukumomi ba, ko wani zayyanan nen tsari na kafa mssarautu ba.
“Dokokin Arewacin ƙasar nan sune mujadalar kafa masarautun gargajiya, duk masarautun da ake dasu a halin yanzu, ba matasa majiya ƙarfi me suka kafa su, ko ‘yan shaci-faɗi ba, ba kuma an kafa sune ta hanyar zubar da jini ko tashin-tashina ba, domin akwai tsari na ‘yanchi, Kuma inda ‘yanchin ka ya ƙare, nan na wasu ke farawa.”
Gwamnan sai ya shaida wa al’ummar Sayawa, “wannan shine zangona na kusan ƙarshe da nake yi maku alfarma, domin farkon shekara Mai zuwa ko ƙarshen ta, zamu zauna a wannan zaure, tare da dukkanin Sayawa masu ruwa da tsaki, inda za mu yi bibiyar rahoton wancan kwamiti ta yadda zamu fito da wani ingantaccen matsayi wanda zai dace da kafa masarautar Sayawa.”
