Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta horar da ma’aikata dabarun samar da kayayyakin gwamnati a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau 

Cibiyar Binciken Siyayyar kayayyakin gwamnati dake Jami’ar Ahmadu Bello Zariya tare da haɗin gwiwar ofishin shugaban ma’aikata na jihar Jihar Zamfara ta horas da wasu zaɓaɓɓun ma’aikatan jihar dubarun hanyoyin samar kayayyakin gwamnati a sauƙaƙe.

Da yake buɗe horaswar, shugaban ma’aikata na jiha Barista Ahmad Liman ya bayyana cewa, horon zai ci gaba da tafiya yadda ya kamata domin inganta tsarin sayan kayayyaki da ayyukan gwamnati hanya mafi inganci da nagari. 

Ya ƙara da cewa za a ci gaba da samar da ingattun kwangiloli bisa ƙa’idojin saye da sayarwa a jihar. 

Ya kuma ba da tabbacin cewa horon zai kasance mai dorewa domin horar da ma’aikatan samar da kayayyaki masu inganci a jihar. 

Shi ma da yake nasa jawabin babban daraktan ofishin kula da harkokin samar da kayayyakin gwamnati na jihar Zamfara Engr.  Bashar Galadima ya jaddada cewar horaswar zai bai wa ma’aikatan jihar haziƙanci da basira da nufin ba su ilimi domin su yi fice a harkar samar da ingattun kayayyakin gwamnati a jihar. 

A nasa jawabin, daraktan cibiyar bincike kan harkokin samar da ingattun kayayyakin gwamnati ta Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, Dakta Ma’awiyya Abubakar, ya bayyana cewa horon an tsara shi ne domin tunkarar muhimman al’amuran da suka shafi harkokin sayo kayayyakin gwamnati a karkashin dokar sayan kayayyaki ta jihar Zamfara ta shekarar 2021.  

“Manufofin horon shine don haɓaka mahalarta don su fahimci hanyoyin samar da nagartattun kayayyaki musamman ta hanyoyin bayar da kwangiloli masu nagarta da inganci,”  Dr. Ma’awiyya ya bayyana.

Hakazalika, ya umurci mahalarta taron da su kasance masu bin gaskiya da sanin ya kamata da kuma sani daraja da kimar kuɗaɗen gwamnati, yayin da ya yaba wa gwamnatin jihar Zamfara bisa haɗin gwiwa da cibiyar binciken samar da kayayyaki ta Jami’ar Ahmadu Bello domin ci gaban jihar.

By ukarofi